COVID-19: Jerin kayan tallafin da FG ta tura jihar Kano bayan ta yi alkawari

COVID-19: Jerin kayan tallafin da FG ta tura jihar Kano bayan ta yi alkawari

- Ma'aikatar walwala da jin kan dan kasa ta tarayya ta tura mota 110 dankare da hatsi don raba wa mabukata da matalautan jihar Kano

- Kamar yadda ministar ma'aikatar, Sadiya Umar Farooq ta bayyana, ta ce daya daga cikin tallafin da gwamnatin tarayyar ta yi alkawari ga jihar shine kayan abinci

- Ta ce ma'aikatarta za ta hada kai da cibiyoyin da ke karkashinta wajen mika duk abinda ya kamata ga jihar don hana yaduwar annobar

Ma'aikatar walwala da jin kan 'yan kasa ta tarayya ta tura motoci 110 na tallafin kayan abinci daga gwamnatin tarayya zuwa jihar Kano.

Ministan walwala da jin kan 'yan kasa, Sadiya Umar Farooq ce ta sanar da hakan a hedkwatar ma'aikatar da ke Abuja.

Ta ce ma'aikatar ta kai tirela 10 shake da shinkafar gwamnati jihar Kano din tun kusan makonni biyu da suka gabata, jaridar Leadership ta ruwaito.

Ta kara da cewa, an tura motocin hatsi 100 zuwa wurare daban-daban na jihar Kano don rabawa ga matalauta da mabukata kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarta.

A ranar Litinin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin rufe jihar Kano din tare da yin alkawarin samar da tallafin duk da jihar za ta bukata.

COVID-19: Jerin kayan tallafin da FG ta tura jihar Kano bayan ta yi alkawari

COVID-19: Jerin kayan tallafin da FG ta tura jihar Kano bayan ta yi alkawari
Source: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: Gawar dan sanda ta kawo firgici da tashin hankali

Kamar yadda jaridar Leadership ta bayyana, Farooq ta ce motocin hatsin na kan hanyar Kano kuma sun kunshi gero, dawa da masara wadanda aka debo daga ma'adanar hatsin kasar nan.

Ministan ta jaddada cewa, daya daga cikin tallafin da gwamnatin tarayyar za ta bada shine tallafin kayan abinci ga mabukata da matalauta a jihohin da annobar ta fada wa.

A don haka ta tabbatar wa shugaban NEMA, Injiniya Mustapha Maihaja cewa: "Ma'aikatar za ta ci gaba da aiki tare da NEMA da sauran cibiyoyin da ke karkashinta don sauke nauyin da ke kanta.

"Sun hada da tabbatar da walwala da jin kan 'yan kasa a gida Najeriya da kuma wadanda ke ketare ballantana a lokacin annobar COVID-19."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel