COVID-19: Gwajin da aka yi wa likitocin China 15 da suka zo Najeriya ya fito

COVID-19: Gwajin da aka yi wa likitocin China 15 da suka zo Najeriya ya fito

Tawagar kwarrarun ma'aikatan Lafiya 15 da suka zo Najeriya daga China domin taimakawa kasar wurin yaki da COVID-19 duk ba su dauke da kwayar cutar a cewa Ministan Lafiya, Osagie Ehanire.

Mr Ehanire yayin jawabin da kwamitin kar ta kwana na shugaban kasa kan yaki da COVID-19 a ranar Talata ya ce sakamakon gwajin da aka yi ya nuna dukkan yan kasar na China ba su dauke da kwayar cutar.

Wannan na zuwa ne bayan sun kwashe kwanaki 14 a killace domin tabbatar da cewa ba su kamu da cutar ba.

COVID-19: An fitar da sakamakon gwajin da aka yi wa likitocin China 15 da suka zo Najeriya

COVID-19: An fitar da sakamakon gwajin da aka yi wa likitocin China 15 da suka zo Najeriya
Source: Twitter

DUBA WANNAN: COVID-19: Sabon salon sallar jam'i a kasashen duniya (Hotuna)

Ya ce, "Batun tawagar kasar China da suka zo, an musu gwaji bayan sun kammala kwanaki 14 a killace. Dukkansu ba su dauke da kwayar cutar.

"Yanzu maaikatar Lafiya ta tarayya ta gama da wannan batun.

"Tawagar kasar Chinan sun iso Najeriya ne a ranar 8 ga watan Afrilu domin musayar ilimi kan yadda suka yi yaki da annobar COVID-19 a kasar su."

Wasu yan Najeriya sun soki matakin na gwamnatin tarayya na gayyato kwararrun inda suke cewa Najariya tana da isasun kwararrun likitoci da za su iya magance annobar na COVID-19 .

Kungiyar Likitocin Najeriya, NMA, itama ta bayyana gayyatar da aka yi wa yan kasar Chinan a matsayin cin fuska da yan kungiyar da sauran ma'aiktan lafiya da ke aiki tukuru domin yaki da cutar a yanayi mai wahala.

Amma Mr Ehanire ya ce yan kasar na China za su bayar da shawarwari ne ga Najeriya a yakin da ta ke yi da annobar COVID-19 tare da sanar da Najeriya yadda kasarsu ta yi maganin cutar.

Shugaban Kamfanin China Civil Engineering Construction Cooperation (CCECC), Jacques Liao ya kuma ce makasudin zuwar tawagar likitocin shine kula wa lafiyar da ma'aikatan CCECC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel