COVID-19: Sabon salon sallar jam'i a kasashen duniya (Hotuna)

COVID-19: Sabon salon sallar jam'i a kasashen duniya (Hotuna)

- Tun bayan bullar annobar Covid-19 a kasashen duniya, masallatai manya na duniya sun daina sallar jam'i tare da rufe duk wasu ayyukansu

- Kamar yadda kasar Saudia ta bayyana rufe manyan masallatai masu daraja guda biyu na kasar, haka sauran manyan masallatan duniya suka yi

- Amma kuma akwai msallatai da yawa har da na kasar Saudi Arabia da ake bari ana sallar jam'i amma cike da dokar nisantar juna

Tun bayan barkewar annobar cutar Covid-19 a duniya ne masallatai manya suka daina sallar jam'i.

Musulmai da yawa tare da gwamnatocin kasashen duniya sun dauka wannan matakin ne don hana yaduwar annobar.

Wannan haramta sallar a jam'in kuwa ya jawo cece-kuce a wurin musulman duniya.

Yayin da wasu suka ki bin dokar, sun dauka matakin dakile cudanya da juna tare da nisantar juna duk da kuwa ana sallar jam'in.

A sabon salon sallar jam'in, babu batun hada kafadu ko kafafu kamar yadda jam'i yake bayyana.

Ga wasu zababbun hotunan yadda ake sallar jam'i a manyan masallatai daban-daban na fadin duniya.

COVID-19: Sabon salon sallar jam'i a kasashen duniya (Hotuna)

Sallar jam'in Juma'a a jihar Jigawa a yayin da suke kiyaye dokar nisantar juna. Hoto daga Twitter
Source: Twitter

COVID-19: Sabon salon sallar jam'i a kasashen duniya (Hotuna)

Wannan hoton an dauke shi ne a ranar 24 ga watan Afirilu a garin Makkah inda wasu malamai ke sallar jam'i. Hoto daga Getty Images
Source: Getty Images

COVID-19: Sabon salon sallar jam'i a kasashen duniya (Hotuna)

Shafin da ke kula da Masallatai biyu masu daraja na kasar Saudi Arabia ya wallafa wannan hoton a ranar ta biyu na watan Ramadana. Hoto daga Facebook
Source: Getty Images

COVID-19: Sabon salon sallar jam'i a kasashen duniya (Hotuna)

Wannan hoton wasu Falasdinawa ne da ke sallara tarawih a wajen Masallacin Aqsa a birnin Jerusalem. Hoto daga Getty Images
Source: Getty Images

COVID-19: Sabon salon sallar jam'i a kasashen duniya (Hotuna)

Hoton wasu malamai ne da ke sallar jam'i a birnin Delhi na kasar Indiya yayin da suke bada tazara ga junansu. Hoto daga Getty Images
Source: Getty Images

COVID-19: Sabon salon sallar jam'i a kasashen duniya (Hotuna)

Wasu Falasdinawa da Isra'ilawa na sallar jam'i yayin da suke bada tazarar mita bibbiyu a tsakaninsu. Hoto daga Getty Images
Source: Getty Images

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Majalisar dattijai ta yi sabon kakaki

COVID-19: Sabon salon sallar jam'i a kasashen duniya (Hotuna)

Musulmai a kasar Nepal suna gabatar da sallar jam'i a Masallacin Kashmeeree. Hoto daga Getty Images
Source: Getty Images

COVID-19: Sabon salon sallar jam'i a kasashen duniya (Hotuna)

Masu bada agaji da taimakon gaggawa sun yi wa abokin aikinsu sallar gawa bayan cutar Korona ta kasheshi a kasar Pakistan. Hoto daga Getty Images
Source: Getty Images

COVID-19: Sabon salon sallar jam'i a kasashen duniya (Hotuna)

Imam Magdy Badr na limanci a kasar Dearbon, suna bada tazara don hana yaduwar cutar Covid-19. Hoto daga Getty Images
Source: Getty Images

COVID-19: Sabon salon sallar jam'i a kasashen duniya (Hotuna)

Babban mai bayar da fatawa na kasar Bosniya yana jagorantar sallar jam'i a ranar Juma'ar farko ta watan Ramadana. Hoto daga Getty Images
Source: Getty Images

COVID-19: Sabon salon sallar jam'i a kasashen duniya (Hotuna)

Musulmai a kasar Indonesia na gabatar da sallar taraweehi a ranar farkon watan Ramadana. Hoto daga Getty Images
Source: Getty Images

A wani labari na daban, shugaban majalisar dattijan Najeriya, Ahmad Lawan ya bayyana sanata daga jihar Osun, Ajibola Basiru a matsayin sabon shugaban kwamitin yada labarai na majalisar.

Basiru zai dasa daga inda Sanata Godiya Akwashiki ta tsaya a matsayin mukaddashin kakakin majalisar.

Ta ci gaba da aiki a matsayin kakakin majalisar dattijan ne tun bayan da aka kwace kujerar Adebayo Adeyeye a kotu.

Akwashiki sanata ce a karkashin jam'iyyar APC daga jihar Nasarawa.

Ba kakakin majalisar kadai zai tsaya ba, zai kasance shugaban kwamitin majalisar na daukar aiki da kwadago.

Sanata Biodun Olujimi ta jihar Ekiti karkashin jam'iyyar PDP ce ta zama shugabar kwamitin majalisar mai kula da 'yan Najeriya da ke kasashen ketare da kuma kungiyoyin taimakon kai da kai.

Lawan ya bada wannan sanarwar ne a yayin tashi zaman majalisar na yau Talata, jaridar Premium Times ta wallafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel