Sakacin da kasar China ta yi ya haifar da yaduwar cutar korona a duniya - Trump

Sakacin da kasar China ta yi ya haifar da yaduwar cutar korona a duniya - Trump

Shugaban Amurka Donald Trump, ya sake nuna yatsa zuwa ga gwamnatin kasar China, da cewa ita tayi sakacin da ya haifar da yaduwar cutar korona a duniya.

Kamar yadda sashen Hausa na BBC ya ruwaito, Trump ya ce kasar China na da ikon hana yaduwar cutar zuwa sauran sassan duniya.

A hakan ne dai shugaban na Amurka ya ce tabbas sai an gudanar da gagarumin bincike domin gano matakan da gwamnatin China ta dauka tun a yayin da cutar korona ta fara bulla a kasar.

Mista Trump bai gushe ba dai yana ci gaba da cewa, kamata ya yi gwamnatin China ta dauki matakai cikin hanzari na hana annobar korona bazuwa daga tushenta.

Shugaban Amurka; Donald Trump
Shugaban Amurka; Donald Trump
Asali: UGC

Furucin shugaba Trump ya zo ne a cikin jawaban da ya gabatar a wani taron manema labarai a makon da muke ciki.

Babu shakka dai annobar coronavirus ta kashe dubban mutane a fadin duniya, tun bayan bullar bakuwar cutar mai shafar numfashi a watan Disamban da ya gabata a garin Wuhan na kasar China.

KARANTA KUMA: Za a yi bincike kan mace-macen Kano - Buhari

Haka kuma babu tantama a baya dai Shugaba Trump ya sha kiran coronavirus ''Yar China'. Sakatarensa na harkokin waje Mike Pompeo yana kira cutar ''Yar Wuhan', abin da ke matukar bata wa gwamnatin China rai.

Trump da sakatarensa sun yi tir da gwamnatin China kan saken da ta yi daga farkon barkewar cutar.

Mun ji cewa Trump ya kirayi shugaban kasa Muhammadu Buhari ta hanyar wayar tarho, inda ya jajanta masa kan halin da Najeriya ta shiga sanadiyar annobar korona.

Ministan Labarai na kasar, Alhaji Lai Muhammad, shi ne ya bayar da shaidar hakan da cewa shugaban na Amurka ya sha alwashin tallafawa Najeriya da na'urorin taimakon yin numfashi da kasar ta ke da matsananciyar bukatarsu saboda sun yi karanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel