Kwamandan Soji ya nada kansa shugaban kasa a Libya

Kwamandan Soji ya nada kansa shugaban kasa a Libya

Kwamanda a rundunar sojoji a kasar Libya, Khalifa Haftar ya nada kansa shugaban kasa bayan samun goyon bayan mutane mafi rinjaye a kasar kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A jawabin da ya yi da aka haska a talabijin a daren ranar Litinin, shugaban na Sojojin Kasar Libya, LNA, ya sanar da cewa babban kwamandan sojojin kasar ya amsa kirar mutane na karbar ragamar mulki a kasar.

A cikin jawabinsa, Haftar ya kara da cewa an soke yarjejeniyar da aka yi da majalisar dinkin duniya, UN, na kafa gwamnatin hadin kai, GNA, da ke da hedkwata a Tripoli bayan kwashe shekaru ana tashe tashen hankula a kasar.

Kwamanda Soji ya nada shugaban kasa a Libya

Kwamanda Soji ya nada shugaban kasa a Libya
Source: Twitter

DUBA WANNAN: COVID-19: Budurwa roki NCDC ta kama mahaifiyarta saboda karya dokar zaman gida a Nasarawa

Ya ce, "Muna sanar da cewa mun karbi amanar da mutane suka mika mana kuma hakan ya kawo karshen yarjejeniyar Skhirat.

"Yarjejeniyar siyasar ya janyo tabarbarewar alamura a kasar. Za mu yi aiki tukuru domin gina hukumomin gwamnati masu dorewa."

Wata majiya daga kasar Rasha ta shaidawa Reuters a ranar Talata cewa ta yi mamakin ganin yadda Haftar ya karbi mulki a kasar.

Ta ce abinda ya fi muhimmanci yanzu shine yan kasar su aiwatar da yarjejeniyar soji da na siyasa da aka cimma a yayin taron Berlin a watan Janairu da taimakon kasashen waje.

Kasar ta Libya ta kasance cikin tashin hankali tun 2011 a lokacin da mutanen kasar tare da goyon bayan Nato suka yi bore tare da hambarar da gwamnatin Muammar Gaddafi.

Wasu yan Libya da masu rike da mulki a sassan kasar suna ganin Haftar zai iya daidaita alamura a kasar.

Wasu kuma na ganin cewa akwai yiwuwar shi da sojojin sa za su iya kafa mulkin kama karya tare da aikata laifukan yaki da kokarin hambarar da gwamnatin da UN ta amince da ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel