Sheikh Yola: An yi rashin babban Malami a Kano

Sheikh Yola: An yi rashin babban Malami a Kano

Har yanzu mutanen Kano na cigaba da zama cikin zulumi sakamakon annobar yawaitar mace - mace da ta bulla a jihar.

Sheikh Tijjani Yola, daya daga cikin limaman babban Masallacin Murtala, ya mutu da safiyar ranar Talata.

An shiga sati na biyu kenan da rahotanni ke sanar da mutuwar fitattun mutane, yawancinsu dattijai, a garin Kano.

Wata majiya mai kusanci da marigayin ta sanar da jaridar 'TheCable' cewa Sheikh Yola ya mutu ne da safiyar ranar Talata a gidansa da ke karamar hukumar Gwale a cikin birnin Kano.

"Ya mutu ne a gidansa da ke unguwar Gwale a cikin birnin Kano da safiyar yau (Talata), kuma an binne shi da misalin karfe 9:00 na safe," a cewar majiyar.

Sheikh Yola: An yi rashin babban Malami a Kano

Sheikh Yola: An yi rashin babban Malami a Kano
Source: Twitter

Wani mazaunin Kano mai suna Abdullahi Umar ya tabbatar da mutuwar babban malamin, inda ya bayyana cewa jama'ar birnin Kano suna cikin damuwa.

DUBA WANNAN: Tashin hankali: Jami'in gwamnati ya bayyana adadin mutanen da su ka mutu a cikin sati daya a Kano

TheCable ta rawaito cewa Uba Adamu, mahaifin Farfesa Abdallah Adamu, shugaban jami'ar NOUN, ya mutu da safiyar ranar Talata.

Adamu Sarawa, tsohon shugaban majlisar dokokin jihar Jigawa, ya mutu a daren ranar Litinin a gidansa da ke Kano.

Kazalika, annobar mutuwar ta dauki ran Halimatu Shittu, tsohuwar shugabar wata kungiyar mata Musulmi a Najeriya (FOMWAN) reshen jihar Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel