Wata Iska mai karfin gaske ta kashe mutane 2 a Taraba, ta lalata gidaje 500

Wata Iska mai karfin gaske ta kashe mutane 2 a Taraba, ta lalata gidaje 500

Wata guguwa mai karfin gaske ta yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu, tare da lalata akalla gidaje guda 500 yayin da ta mamaye wasu garuruwa 5 a karamar hukumar Gassol, jahar Taraba.

Daily Trust ta ruwaito iskar ta barnata gidaje fiye da 500 da suka hada da makarantu, Coci-coci, wanda hakan yasa ake ganin ba’a taba samun irin wannan guguwar ba a jahar.

KU KARANTA: An kama matar da ta halaka uwar mijinta bayan ta caka ma ta wuka a jahar Neja

Guguwar ta tashi ne da misalin karfe 5 na yammacin lahadi a garuruwan Sabongid, Tella, Takai, Tisol duk a cikin karamar Gassol.

Baya ga gidaje da guguwar ta yi awon gaba dasu, ta yi sanadiyyar asarar dimbin dukiya da suka hada da kayan abinci, dabbobi, kayan amfanin gida da kudinsu ya haura miliyoyin nairori.

Wata Iska mai karfin gaske ta kashe mutane 2 a Taraba, ta lalata gidaje 500
Wata Iska mai karfin gaske ta kashe mutane 2 a Taraba, ta lalata gidaje 500
Asali: Facebook

A yanzu haka yawancin wadanda wannan ibtila’i ya shafa sun koma kwana a waje sakamakon rashin samun tallafin kayan agaji daga gwamnati.

Wani daga cikin mutanen da abin ya shafa, Alhaji Muktar Ajiju Sabongida ya bayyana cewa duka gidajen dake Sabongida sun fuskanci wannan matsala.

Ajuji yace iskar ta lalata makarantarsa, gidansa da kuma gidan yaransa. Ya kara da cewa wata mata ta mutu a wani cocin Katolika dake garin a lokacin da dakinta ya fada mata.

An kuma samu karin mutum daya da ya mutu a garin Takai, duk a sanadiyyar guguwar.

Ajuji yace ba su taba fuskantar irin wannan guguwar a nan kusa ba, don haka ya nemi gwamnatin jahar ta agaza musu.

A wani labarin kuma, gwamnatin jahar Kano ta ce ta gano dalilan da suka kawo mace macen da aka dinga samu a jahar a makon da ta gabata.

A cewar gwamnatin jahar, mace macen na da alaka da cututtukan hawan jini, ciwon siga, sankarau da kuma cutar zazzabib cizon sauro da suka dade suna addabar jama’an jahar.

Gwamnatin yace sun gano haka ne bayan gudanar da cikakken bincike game da mace mace, don haka yace mace macen basu da alaka da Coronavirus, saboda haka kada jama’a su firgita.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: