Dan Atiku ya warke daga coronavirus bayan kwanaki 40 a killace

Dan Atiku ya warke daga coronavirus bayan kwanaki 40 a killace

Dan tsohon mataimakin shugaban kasa, Mohammed Atiku Abubakar, ya sanar da cewar ya warke daga cutar Coronavirus, bayan ya shafe tsawon kwanaki 40 yana fama da cutar.

Jaridar Premium Times ta ruwaito inda Mohammed ke fadin cewa: “A yau ne aka yi mani gwaji na biyu da ya nuna bana dauke da cutar COVID-19.

“Yanzu haka ana shirin sallama na ne, idan Allah ya yarda zan isa gida da yammacin yau.”

Mohammed Atiku dai ya killace kansa bayan an tabbatar da yana dauke da cutar Coronavirus a ranar 19 ga watan Maris.

Dan Atiku ya warke daga coronavirus bayan kwanaki 40 a killace

Dan Atiku ya warke daga coronavirus bayan kwanaki 40 a killace
Source: Twitter

Ya kasance mutum na farko da aka ba da rahoton yana dauke da cutar a Abuja.

Har ila yau Mohammad mai shekara 31 na daya daga cikin mutanen da suka dade ba su warke ba, tun bayan samun bullar cutar da aka yi a kasar.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Emmanuel ya koka game da ingancin abincin da gwamnatin tarayya take rabawa

Hukumar dake yaki da cutuka masu yaduwa a Najeriya NCDC ta ruwaito cewa akwai sama da mutum 1,000 dake dauke da cutar, yayin da tuni ta hallaka mutum 40, 239 kuma suka warke.

A gefe guda mun ji cewa, likafar annobar cutar korona na ci gaba a Najeriya duk da irin kai komo da mahukuntan lafiya ke yi babu dare babu rana domin dakile yaduwar cutar a kasar.

A halin yanzu an samu bullar cutar korona a jihohi 33 na Najeriya ciki har da babban birnin tarayya kamar yadda alkaluman cibiyar dakile yaduwar cututtuka a kasar NCDC suka tabbatar.

Taskar bayanai ta NCDC a ranar Lahadi 26 ga watan Afrilun 2020, ta ce cutar corona ta harbi mutane 1273 yayin da tuni mutum 239 suka warke.

Ya zuwa yanzu dai mutane 40 cutar ta hallaka a fadin Najeriya kamar yadda kididdigar alkaluman ta tabbatar.

Da misalin karfe 11.50 na daren ranar Lahadi, cibiyar mai fafutikar dakile yaduwar cututtuka ta sanar da cewa an samu karin mutane 91 da cutar covid-19 ta harba a fadin Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel