An kama 'yan gudun hijira daga Kano zasu shiga Kaduna a boye a cikin motocin dako (Hotuna)
Jami'an tsaro tare da hadin gwuiwar jami'an gwamnatin Kaduna sun kama wasu manyan motocin dakon kayan abinci da aka boye mutane a cikinsu.
An kama motocin ne ranar Litinin a kauyen Sabon Gida da ke yankin karamar hukumar Ikara yayin da suke kokarin shiga jihar Kaduna.
Manyan motocin sun yi yunkurin shiga jihar Kaduna ne ta iyakarta da karamar hukumar Kiru ta jihar Kano.
Motocin sun yi basaja a zuwan sun dauko kayan abinci ne da zasu kai jihar Kaduna.
Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida a jihar Kaduna, ya ce jami'an tsaro sun kama motocin yayin da suke rangadin tabbatar da dokar hana zirga-zirga.
"Sun sabawa dokar hana zirga-zirga, kamar yadda kowa zai iya gani. Mun samu mutane da yawa da aka boye a cikin manyan motocin.
"Mun yi nasarar kamasu kafin su shiga cikin jihar Kaduna, kuma za mu mayar dasu inda suka fito," a cewar Aruwan.
"Kazalika, mun mayar da wasu dumbin fasinjoji da muka kuma. Za mu cigaba da tabbatar da cewa jama'a sun yi biyayya ga umarnin gwamnatin jihar Kaduna.
"Mu na fuskantar kalubale a kauyuka, inda jama'a ke dukan jami'an tsaro yayin da suke aikin tabbatar da dokar zaman gida.
"Za mu fara amfani da babura domin shiga irin wadannan kauyuka don tabbatar da cewa sun yi biyayya ga umarnin hukuma," a cewarsa.

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter
A yau, Litinin, ne gwamnatin Kaduna ta sanar da cewa an samu kwayar cutar covid-19 a jikin wasu almajirai biyar da gwamnatin jihar Kano ta mayar jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinar lafiya ta jihar Kaduna, Dakta Amina Mohammed-Baloni.
DUBA WANNAN: Tashin hankali: Mutane fiye da 600 sun mutu a cikin sati daya a Kano - Jami'in gwamnati
A cewar sanarwar, wacce gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya wallafa a shafinsa na tuwita, kwamishinar ta bayyana cewa adadin ma su dauke da cutar covid-19 a jihar Kaduna ya koma mutane 9.
Dakta Baloni ta bayyana cewa an mayar da almajiran zuwa cibiyar duba cututtuka ma su yaduwa, wacce ke zaman cibiyar killacewa ta jihar Kaduna.
Kazalika, ta sanar da cewa ana duba lafiyar almajiran kamar yadda ake duba lafiyar duk wanda aka tabbatar yana dauke da kwayar cutar.
Ta bayyana cewa an killace sauran almajiran da ake zargin zasu iya harbuwa daga abokansu da aka samu da kwayar cutar, kuma ma'aikatan lafiya na cigaba da sa-ido a kansu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng