Tallafin annobar covid-19: Aisha Buhari ta aika tireloli 16 makare da magunguna da kayan abinci (Hotuna)

Tallafin annobar covid-19: Aisha Buhari ta aika tireloli 16 makare da magunguna da kayan abinci (Hotuna)

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari, ta bayar da tallafin tireloli 16 makare da kayan abinci da magunguna domin rabawa gidajen talakawa 500,000 a jihar Kano.

Bayan kayan abinci da magunguna, Aisha Buhari ta bayar da tallafin kayan sakawar jami'an lafiya da ke aikin yaki da annobar cutar covid-19 a jihar Kano.

Ta aika kayayyakin ne a matsayin tallafi ga mutanen jihar da aka tilastawa zaman gida tare da nuna tausayawarta ga annobar yawaitar mace - macen jama'a da ta bulla a jihar.

Alhaji Hadi Uba, hadimin Aisha Buhari, shine ya wakilceta yayin mika tallafin ga gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin.

Ya bayyana cewa za a ajiye magungunan a asibitin Muhammadu Buhari domin bawa talakawa kyauta idan an rubuta musu magani yayin da basu da lafiya.

Ya ce, " za a raba kayan abinci da suka hada da shinkafa, taliya, madara, man girki ga gidajen talakawa 500,000. Gidauniyar Aisha Buhari za ta hada kai da gwamnati wajen rabon tallafin."

DUBA WANNAN: Tashin hankali: Jami'in gwamnati ya bayyana adadin mutanen da suka mutu a cikin sati daya a Kano

A yau, Litinin, ne ake saka ran shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai sanar da kunshin tallafin da gwamnatin tarayya za ta bawa jihar Kano.

Ana tsammanin shugaba Buhari zai sanar da hakan ne a cikin jawabin da zai gabatar kai tsaye ga 'yan kasa da misalin karfe 8:00 na dare.

Gwaman Abdullahi Umar Ganduje, ya yi korafin cewa gwamnatin tarayya ta yi watsi da jihar Kano yayin da jama'a ke cigaba da mutuwa a kullum.

Tallafin annobar covid-19: Aisha Buhari ta aika tireloli 16 makare da magunguna da kayan abinci (Hotuna)
Tallafin annobar covid-19
Asali: Twitter

Tallafin annobar covid-19: Aisha Buhari ta aika tireloli 16 makare da magunguna da kayan abinci (Hotuna)
Tallafin Aisha Buhari
Asali: Twitter

Tallafin annobar covid-19: Aisha Buhari ta aika tireloli 16 makare da magunguna da kayan abinci (Hotuna)
Tallafin annobar covid-19
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng