Mutuwar mutane: Lamarin ya na bani tsoro, FG ta yi watsi da Kano - Ganduje ya magantu

Mutuwar mutane: Lamarin ya na bani tsoro, FG ta yi watsi da Kano - Ganduje ya magantu

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi korafin cewa kwamitin shugaban kasa a kan yaki da annobar COVID-19, ta yi wasti da jaharsa a yaki da take yi da cutar, inda ya ce halin da jahar ke ciki abun tsoro ne.

A wata hira da aka yi da shi wanda jaridar Premium Times ta ruwaito, Ganduje ya ce: “Muna cikin babbar matsala.

"Zan iya cewa da kai wannan hali a yanzu haka dai gaskiya ba shi da kyau kuma abin tsoro ne. Saboda babban abin da muka dogara da shi a kokarin dakile corona shi ne cibiyar gwaji.

“Wannan cibiya ta dakatar da ayyukanta kusan kwanaki biyar zuwa shida da suka gabata.

Mutuwar mutane: Lamarin ya na bani tsoro, FG ta yi watsi da Kano - Ganduje ya magantu

Mutuwar mutane: Lamarin ya na bani tsoro, FG ta yi watsi da Kano - Ganduje ya magantu
Source: Twitter

"Kayan da ma ake daukan samfurin a kai Abuja sun yi karanci, kuma ba kaya ne wanda gwamnati za ta je kasuwa ta saya ba. Wadanda aka dau samfurinsu ba su san matsayinsu ba. Za su ci gaba da hulda da mutane."

Gwamna Ganduje ya ci gaba da cewa "Saboda haka wannan babbar matsala ta kwamitin shugaban kasa na Abuja, shi kansa babban daraktar NCDC ya zo nan Kano ya kwana, to amma tun da ya tafi ba mu sake jin duriyarsa ba.

"Shi ma ministan lafiya ya san cewa wannan dakin gwaji ba ya aiki, amma ba mu sake jin komai ba."

Gwamna Ganduje ya kara da cewa baya ga karancin cibiyoyin gwaji a Kano, jihar ba ta samun isassun kayan da za a yi gwajin da su wadanda ya ce gwamnatin tarayya ce kadai ke samar da su.

KU KARANTA KUMA: Covid-19: Ministan lafiya ya sanar da lokacin da cibiyar gwaji za ta dawo aiki a Kano

"Wani abin takaicin ma shi ne kwalaben da za a sa wannan samfurin babu su isassu, kuma ba za a iya sa wa a cikin wani waje ba in ba wadannan kwalabe ba.”

A wani labarin kuma, mun ji cewa shugaban BUA, Alhaji Abdul Samad Rabiu, ya sanar da sake bayar da tallafin naira biliyan N3.3 ga jihohin Kano da Lagas da kuma kwamitin shugaban kasa don yaki da annobar COVID-19.

Rabiu ya damu matuka da hauhawan masu dauke da kwayar cutar coronavirus, musamman a Kano da Lagas, duk da kokarin da ake na hana yaduwar cutar, a cewar wata sanarwa da ta fito daga BUA a ranar Lahadi.

Tallafin kari ne a kan gudunmawar da kamfanonin BUA ta bayar a farko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel