Sauran kiris mu wajabta amfani da takunkumin rufe fuska a Kano - Ganduje

Sauran kiris mu wajabta amfani da takunkumin rufe fuska a Kano - Ganduje

A yayin da adadin wadanda annobar corona a jihar Kano ta kai 77, baya ga dakatar da gwajin gano masu dauke da cutar a jihar, gwamna Abdullahi Ganduje ya shimfida wata sabuwar doka.

Babu shakka jihar Kano na ci gaba da kasancewa babban kalubale na yaki da cutar coronavirus a fadin Najeriya. Sai dai fa duk da hakan gwamnan jihar na ganin akwai alamun nasara.

A fafutikar da ake yi na dakile yaduwar cutar, gwamna Ganduje ya jaddada muhimmancin amfani da takunkumin rufe fuska kamar yadda mahukuntan lafiya suka shar'anta.

Gwamna Ganduje ya ce nan ba da jimawa ba za a tursasawa dukkanin al'ummar jihar Kano amfani da takunkumin rufe fuska domin hana yaduwar cutar.

A sanadiyar haka gwamnatin Kano ta dukufa wajen samar da takunkuman rufe fuska miliyan daya domin ci gaba da daukan matakai na dakile annobar corona.

Gwamnan Kano; Abdullahi Ganduje
Gwamnan Kano; Abdullahi Ganduje
Asali: Twitter

A bangaren tabbatar da yiwa gwamnatin biyayya a kan dokar kulle da hana fita da ta shimfida a jihar, gwamna Ganduje ya ce an kirkiri kotukan tafi-da-gidanka guda goma domin hukunta wadanda za su sabawa dokar.

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta bayyana muhimmancin takunkumin rufe hanci da baki da cewar yana bayar da kariya daga kamuwa da cutar corona.

KARANTA KUMA: Zafafan hotuna 15 na Rahama Sadau da 'yan uwanta mata uku

WHO ta ce takunkumin yana iya hana kwayoyin cutar da ke fitowa daga baki ko hancin masu dauke da cutar su isa zuwa ga masu lafiya.

A halin yanzu dai mutane 1273 cutar corona ta harba a duk fadin Najeriya kamar yadda taskar bayanai ta hukumar dakile yaduwar cututtuka a kasar, NCDC, ta fitar.

Har ila yau kuma jihar Legas ce a kan sahu na gaba ta fuskar yawan wadanda cutar ta kama inda adadinsu ya kai 731, sai kuma birnin tarayya inda cutar ta harbi mutum 141 yayin da jihar Kano ta biyo baya da mutum 77.

Mun ji cewa gwamnan Kano, ya nemi gwamnatin tarayya da ta kawo masa dauki na tallafin kudi har naira biliyan 15 da zai taimakawa jihar wajen yakar wannan annoba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel