Abdulsamad ya sake bayar da tallafin fiye da biliyan uku don yaki da annobar covid-19

Abdulsamad ya sake bayar da tallafin fiye da biliyan uku don yaki da annobar covid-19

Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Alhaji Abdul Samad Rabiu, ya sanar da sake bayar da tallafin naira biliyan N3.3 ga jihohin Kano da Lagas da kuma kwamitin shugaban kasa don yaki da annobar COVID-19.

Rabiu ya damu matuka da hauhawan masu dauke da kwayar cutar coronavirus, musamman a Kano da Lagas, duk da kokarin da ake na hana yaduwar cutar, a cewar wata sanarwa da ta fito daga BUA a ranar Lahadi.

Tallafin kari ne a kan gudunmawar da kamfanonin BUA ta bayar a farko.

Har ila yau mai kudin Afrika wanda ya kasance haifaffen Kano, Aliko Dangote, ya gina cibiyar killace masu cutar covid-19 a filin wasa na Sani Abacha sannan ya bayar da ita ga gwamnatin Kano.

A ranar 26 ga watan Maris, 2020, Rabiu ya sanar da bayar da tallafin naira biliyan daya ta hannun gidauniyar BUA, don karfafa kokarin da gwamnati ke yi na yakar annobar COVID-19.

Abdulsamad ya sake bayar da tallafin fiye da biliyan uku don yaki da annobar covid-19

Abdulsamad ya sake bayar da tallafin fiye da biliyan uku don yaki da annobar covid-19
Source: UGC

Ya kuma yi alkawarin bayar da tallafin kayan asibiti da suka hada da akwatin gwaji da kayan kariya na likitoci ga jihohi tara a Najeriya.

Kwana daya da fadin hakan, BUA ta cika alkawarinta ta hanyar tura kudin zuwa asusun tallafin COVID-19 a Babban bankin Najeriya.

Wata sanarwa daga sashin sadarwan na BUA ta ce, gidauniyar ta kuma bayar da tallafin miliyan 300 zuwa ga jihohin Sokoto, Edo da Ogun domin taimaka masu wajen shirin yaki da annobar COVID-19.

Da yake sanar da sabon tallafin zuwa ga Lagas da Kano, Rabiu ya ce "Kano, wacce ta samu hauhawan masu cutar a baya-bayan nan, ciki harda mutuwar daruruwan mutane da ba a san dalili ba, za ta samu biliyan biyu.

"Sannan Lagas wacce ke da mafi yawan wadanda suka kamu a Najeriya za ta samu biliyan daya."

Ya ce naira miliyan 300 kuma zai tafi asusun kwamitin shugaban kasa a kan yaki da cutar.

KU KARANTA KUMA: Majalisar wakilai ta gimtse hutun da ta tafi bayan barkewar annobar covid-19

Rabiu ya ce za a kafa wata kungiya da za ta hada da kwamitin shugaban kasa a kan cutar, hukumar kula da yaki da cututtuka (NCDC) da sauran masu ruwa da tsaki a jihohin Kano da Lagas.

Za a kafa kungiyar ne domin su kula da yadda za a kashe sabon tallafin da gidauniyar BUA ta bayar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel