Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya lalata gidaje 271 a jahar Kaduna
Wani mamakon ruwan sama da ya sauka a karamar hukumar Sanga ta jahar Kaduna a ranar Juma’a, 24 ga watan Afrilu ya lalata gidajen jama’a da dama.
Jaridar Punch ta ruwaito ruwan ya tafka barnar ne a garuruwa guda 6 dake karamar hukumar, kamar yadda shugaban karamar hukumar, Charles Danladi ya bayyana a ranar Lahadi.
KU KARANTA: Mace mace a Kano: Mahaifiyar shugaban hukumar DSS ta rasu a Bichi
Ciyaman Danladi ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru a garin Kafanchan, inda yace lamarin ya faru ne a ranar Juma’a.
Shugaban karamar hukumar ya bayyana garuruwan da lamarin ya shafa kamar haka; Aboro, Sabon Gida, Ungwan Bera, Janda, Ungwan Goma, da kuma Kurmin Goro.

Asali: UGC
“Muna tunkarar damina ne a yanzu, kuma tun yanzu ruwa ya lalata gidajen jama’a da dama, ina matukar tausaya musu, musamman idan aka duba halin da ake ciki. Ruwan ya dauke rufin wata makaranta gaba daya.
“Yayin da wasu kuma shagunansu ne suka yi asarar su, amma dai babu wanda ya rasa ransa a sanadiyyar lamarin, sai dai wasu sun samu rauni, kuma a yanzu haka suna samun kulawa a asibiti.
“Na umarci daraktan ayyuka na karamar hukumar ya zagaya garuruwan da lamarin ya shafa domin gano iya asarar da suka yi don samin yadda zamu taimaka musu da tallafi.” Inji shi.
A hannu guda kuma, gwamnatin jahar Kano ta bakin kwamishinan watsa labarunta, Muhammad Garba ta ce ta gano dalilan da suka kawo mace macen da ake ta samu a jahar.
Idan za’a tuna a makon da ta gabata ne dai aka dinga samun mace macen mutane a jahar Kano sakamakon wani dalili ko wata cuta da ba’a san tabbacinsa ba.
A cewar gwamnatin jahar, mace macen na da alaka da cututtukan hawan jini, ciwon siga, sankarau da kuma cutar zazzabin cizon sauro da suka dade suna addabar jama’an jahar.
Garba yace sun gano haka ne bayan sun gudanar da cikakken bincike game da mace mace, don haka yace mace macen basu da alaka da Coronavirus, saboda haka kada jama’a su firgita.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng