Mutum biyu sun yi layar zana a jihar Borno bayan sakamakon gwaji ya nuna suna da covid-19
Kwamitin ko ta kwana da gwamnatin jihar Borno ta kafa domin yaki da annobar cutar covid-19 ya bukaci mazauna Maiduguri su ankara a yayin da wasu ma su dauke da kwayar cutar covid-19 su ka gudu.
Kwamishinan lafiya a jihar Borno, Dakta Salisu Kwaya-Bura, ne ya sanar da hakan ranar Lahadi a Maiduguri, yayin da ya ke gabatar da jawabi ga manema labarai a kan annobar cutar covid-19 a jihar Borno.
Ya ce mutanen biyu; namiji mai shekaru 24 da mace mai shekaru 42, sun tsere don kar a kaisu cibiyar killacewa, kuma har yanzu ba a san inda suke ba.
Kwaya-Bura, sakataren kwamitin ko ta kwana, ya ce an baza wata tawagar jami'ai na musamman domin nemo mutanen tare da kaisu cibiyar killacewa.
"Da farko shi namijin ya amsa kiran wayar da kwamitinmu ya yi masa bayan an dauki jininsa domin gudanar da gwaji, amma daga baya sai ya kashe wayarsa bayan ya fuskanci cewa sakamako ya nuna yana dauke da kwayar cutar.
"Duk lokacin da aka dauki jinin mutane domin yi musu gwaji, mu kan basu shawarar su killace kansu har sai sakamakonsu ya fito.

Asali: Twitter
"Mu na daukan adireshinsu da lambobin waya domin tuntubarsu bayan fitowar sakamakon gwaji. Wannan shine tsarin da muke aiki da shi.
"Doka ba ta yarda a tsare wanda ake zargin ya yi mu'amala da mai dauke da kwayar cutar covid-19 ba. Ba mu da ikon yin hakan.
DUBA WANNAN: An sallami dukkan wadanda cutar covid-19 ta harba a garin da annobar ta samo asali a China
"Mu na basu damar su tafi, amma bisa sharadin cewa za su killace kansu, sannan za a mayar dasu cibiyar killacewa idan sakamakon gwaji ya nuna da akwai bukatar hakan.
"Amma duk da haka, matashin ya zabi ya gudu, ya buya," a cewar kwamishina Kwaya-Bura.
Kwaya-Bura ya yi kira ga ma su dauke da kwayar cutar covid-19 a kan su sani cewa kamuwa da kwayar cutar ba ya nufin cewa karshen rayuwar mutum ta zo.
Kwamishinan ya bayyana cewa yanzu haka suna da mutane 19 da ke jinyar cutar covid-19 a cibiyar killacewa da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
A cewar Kwaya-Bura, mutane 16 ne su ka kamu da kwayar cutar covid-19 bayan ta yadu cikin jama'a, yayin da ake bibiyar wasu mutane 14 da aka tabbatar sun yi mu'amala da ma su dauke da kwayar cutar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng