Annobar COVID: Gwamnan Ebonyi ya ce ba zai rufe jiharsa ruf ba

Annobar COVID: Gwamnan Ebonyi ya ce ba zai rufe jiharsa ruf ba

Ganin yadda annobar cutar COVID-19 ta ke cigaba da kashe Bayin Allah, gwamnan jihar Ebonyi watau Mista David Umahi ya yi magana game da takunkumin hana mutanen gari fita.

Gwamna Dave Umahi ya bayyana cewa ba zai rufe jiharsa tsaf ba duk da halin da aka shiga ciki a Najeriya. A halin yanzu dai akwai dokar hana fita da sassafe da kuma yamma a jihar.

Gwamnatin Ebonyi ta dauki matakin haramta zirga-zirga a wasu lokutan rana domin takaita yaduwar cutar COVID-19. Gwamnatin ta ce ba za ta dauki matakin da ya wuce wannan ba.

Dave Umahi ya ce ba zai garkame jihar gaba daya ba, Umahi yi magana ranar Lahadi, inda ya ce tsaya ya yi la’akari da yanayin karfin tattalin jihar Ebonyi kafin ya dauki wannan mataki.

“Na yi la’akari da alkaluman talaucin jihar Ebonyi, don haka na ke kira ga masu bada shawarar a rufe dukkanin kasuwanni da su sake duba wannan magana da su ka kawo.” Inji Umahi.

KU KARANTA: Gwamnan Anambra ya bada iznin bude kasuwani a cigaba da ciniki

Annobar COVID: Gwamnan Ebonyi ya ce ba zai rufe jiharsa ruf ba

Gwamnan Ebonyi ya sa sharadin dawo da acaba a watan gobe
Source: Depositphotos

“Ba mu da wanda ya kamu da cutar COVID-19, a dalilin haka babu bukatar rufe hanyoyin neman kudin mutanenmu.” Mai girma gwaman ya yi wannan jawabi ne jiya a garin Abakaliki.

Mista Umahi ya fitar da wannan jawabi ne ta bakin kwamishinan yada labarai da wayar da kai na jihar, Uchenna Orji. Gwamnan ya godewa jama’a da irin hakurin da su ka yi da hukuma.

“Yadda jama’a su ke bin dokar hana fitan da mu ka sa ya nuna kokarin da shugabannin kananan hukumomi da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki su ke yi wajen yaki da annobar."

Ina kan ra’ayin cewa idan har zuwa 1 ga watan Mayu, 2020, babu wanda ya kamu da wannan cuta a Ebonyi, za mu cire takunkumi hana fita tsakanin karfe 7:00 na dare zuwa na safiya."

“Za mu cire dokar hana acaba a ranar 1 ga watan Mayu idan ba a samu cutar ba.” Gwamnan ya ce za a tabbatar da dokar tazara, sannan ya fadi irin kokarin da gwamnatin tarayya ta yi a jihar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel