Masassara da hawan jini su ke kashe mutane ba COVID-19 ba – Gwamnatin Kano

Masassara da hawan jini su ke kashe mutane ba COVID-19 ba – Gwamnatin Kano

Daga karshe, gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta fito ta jajantawa jama’anta tare da amincewa da ikirarin karuwar mace-macen da ba a saba ganin irinsa ba a wannan lokaci.

Gwamnatin jihar ta kwatanta lamarin da abin alhini da tashin hankali. Jaridar TheCable ta rahoto yadda mace-mace ke yawaita a jihar a yayin da ake tsakiyar annobar cutar COVID-19.

Amma kuma Gwamna Abdullahi Ganduje ya musanta lamarin tare da cewa akwai zuzutawar mutane. Ana dai rade-radin fiye da mutane 600 su ka mutu a cikin makon da ya gabata.

A wata takarda da gwamnati ta fitar a ranar Lahadi, kwamishinan yada labarai, Muhammad Garba, ya ce gwamnatin jihar na kokarin ganin yadda za ta tsare rayukan mutanen Kano.

Kwamishinan labaran ya ke cewa gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta samu matukar jinjina daga cikin gida da waje a kan matakan da ta dauka na hana yaduwar cutar Coronavirus.

KU KARANTA: Shararren Farfesan ilmin koyar da aikin jarida ya mutu a Kano

Masassara da hawan jini su ke kashe mutane ba COVID-19 ba – Gwamnatin Kano
Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta sha alwashin ceto ran al'umma
Asali: Twitter

"Wannan kokarin ne ya ke bayyana yadda duk da Kano ta ke da tarin jama'a, amma cutar ba ta bulla ba sai kwanan nan.” A yanzu mutane fiye da 77 su ke dauke da COVID-19 a Kano.

Garba ya ce: "Duk da mun amince cewa halin da jihar a yanzu ke ciki abin dubawa ne, amma ba za mu sare ba sai mun tabbatar mun kare lafiyar mazauna jihar daga annobar COVID-19.”

Gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta bayyana cewa wasu cututtuka daban ne su ke yin sanadiyyar mutuwar mutane. Daga ciki akwai hawan jini da kuma zazzabin ciwon sauro.

Hakan na zuwa ne bayan gwamna Ganduje ya umarci ma’aikatar lafiya ta jihar ta binciki musababbin mutuwan da ake yi a jihar Kano. Mafi yawan masu mutuwar dai tsofaffi ne.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel