Ana zargin gwamnatin Akwa-Ibom da korar Likita a kan yiwa mutane gwajin COVID-19

Ana zargin gwamnatin Akwa-Ibom da korar Likita a kan yiwa mutane gwajin COVID-19

A jihar Akwa Ibom, shugaban kungiyar likitoci na NMA watau Dr. Aniekeme Uwah ne ya ke kan gaba wajen yaki da cutar COVID-19. A karshen makon jiya kwatsam aka ji an tsige shi.

Jaridar Premium Times ta fitar da wani rahoto a ranar 26 ga watan Afrilu, 2020, ta jefi gwamnatin jihar Akwa Ibom da tsige wannan kwararren Likita daga aiki saboda wani sabani da aka samu.

Rade-radi sun fara karada shafukan sada zumunta cewa an yi waje da wannan likita ne saboda ya amince ayi wa mutane fiye da yadda gwamnati ta ke bukata gwajin kwayar cutar COVID-19.

Wasu hadiman gwamna Udom Emmanuel sun yi kokarin wanke gwamnati daga badakalar tsige wannan babban likita amma a karshe su ka damalmala lamarin da wasu hujjojin so-ki-burutsu.

A ranar Asabar da ta wuce ne mai magana da yawun kungiyar NMA a Akwa Ibom, Emmanuel John, ya shiga gidan rediyo aka yi hira da shi, ya bayyana abin da ya sani game da rikicin.

“A lokacin da kwamishinan lafiya ya kira Dr. Aniekeme Uwah ya fada masa cewa ka da ya yi wa mutane fiye da goma gwaji, har Dr. Uwah ya gwada mutane 19.” Inji Dr. Emmanuel John.

KU KARANTA: Azumin Ramadan ya na karawa mutane lafiya inji wani Likita

Ana zargin gwamnatin Akwa-Ibom da korar Likita a kan yi mutane gwajin COVID-19
Mai girma gwamnan jihar Akwa-Ibom Udom Emmanuel a ofis
Asali: Facebook

Kakakin NMA ya ce: “Mutum na 20 da za a yi gwaji a lokacin da aka kira shi, wani babban likitan koda ne wanda ya hadu da masu cutar COVID-19, kuma yanzu haka ya killace kansa.”

Ya ce: “Abin da Dr. Uwah ya yi na yi wa mutane 31 gwaji ya ceci jihar nan daga abin kunya. Ya kuma ceci al’ummar nan daga kamuwa da cuta da ace mutanen nan su na dauke da ita.”

Mai magana da yawun kungiyar likitocin ya ce wadanda aka yi wa gwaji sun cancanta, don haka babu dalilin da likitan zai bukaci su koma gida ba tare da an yi masu gwajin cutar ba.

“Idan aka samu siyasa ta shiga cikin lamarin gwaji, wannan abin kunya ne. Ba za mu karbi wannan ba. A harkar kiwon lafiya, wannan shi mu ke cewa abin da bai dace ba.” Inji John.

Da aka tambaye sa ko akwai dalilin kin yi wa wasu gwaji sai ya ce akwai jihohin da ke yin hakan, amma wannan abu ne da bai dace ba. “A kan me za a yi wa wani gwaji, a kyale wani?”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel