Ministocin Buhari sun bullo da sabuwar tsirfa a kan nada madadin marigayi Abba Kyari

Ministocin Buhari sun bullo da sabuwar tsirfa a kan nada madadin marigayi Abba Kyari

Wasu daga cikin mambobin majalisar zartarwa (FEC) sun fura kulle ganin yadda za su cicciba daya daga cikinsu da zai zama madadin marigayi Abba Kyari, tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.

'TheNation' ta rawaito cewa tuni wasu daga cikin ministocin sun fara tuntubar wasu makusanta shugaba Buhari domin su lallaba shi ya dauki daya daga cikinsu a matsayin wanda zai maye gurbin Kyari.

Jaridar ta bayyana cewa shugaba Buhari yana jiran a gama zaman makoki da jimamin mutuwar Abba Kyari kafin ya nada madadinsa.

Sai dai, jam'iyyar APC ta bayyana cewa ba zata shiga cikin batun wanda Buhari zai zaba domin maye gurbin marigayi Abba Kyari ba.

Wata majiya ta bayyana cewa ministocin na son Buhari ya dauki daya daga cikinsu ne saboda samun saukin aiki da shi, musamman saboda fahimtar junansu da suka yi.

Kazalika, suna ganin cewa daukan daya daga cikinsu zai kore duk wani jinkirin koyon aiki da sabawa da mambobin FEC da za a iya fuskanta idan Buhari ya nada wani na waje.

Sai dai, babu tabbatacin cewa shugaba Buhari zai amince da wannan mataki na ministocinsa duk da wata majiya ta tabbatar da cewa dan arewa Buhari zai sake nadawa.

Ministocin Buhari sun bullo da sabuwar tsirfa a kan nada madadin marigayi Abba Kyari

Wasu ministocin Buhari
Source: Twitter

Ministoci da mambobin FEC da ake saka ran Buhari zai iya nadawa sun hada da; Adamu Adamu (ministan ilimi, sannan makusancin Buhari); Sakataren gwamnatin tarayya, Mr. Boss Mustapha; ministan albarkatun ruwa, Suleiman Adamu.

Ministan sufurin samaniya (Aviation), Sanata Hadi Sirika; babban mataimaki ga Buhari a bangaren aiyuka na musamman, Ya’u Shehu Darazo; ministan shari'a, Abubakar Malami (SAN).

Sauran sune; ministar walwala da tallafi, Sadiya Umar Farouq; ministan sufuri, Rotimi Amaechi; da ministan aiyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola.

DUBA WANNAN: Covid-19: FG ta yi magana a kan yiwuwar sake bude makarantu

"Duk da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa makusanci ne wurin shugaban kasa, tuni wasu ministoci sun shiga zawarcin kujerar.

"Su na ganin cewa daukan daya daga cikinsu zai saukaka 'yar tsamar aiki da ake samu a tsakanin mambobin FEC, sannan zai kara karfafa alakar da ke tsakanin shugaban kasa da ministocinsa," a cewar majiyar.

Majiyar ta bayyana cewa, "ba wai sun zabi wani mutum guda da suke so shugaba Buhari ya nada ba ne, burinsu shine shugaban kasa ya dauki daya daga cikinsu.

"Har yanzu shugaban kasa bai yi magana ko nuna wata alama a kan wanda zai nada a matsayin marigayi Kyari ba."

Da aka tambayi majiyar a kan yankin da shugaba Buhari zai zabi madadin marigayi Kyari, sai ya kada baki ya ce, "tabbas daga arewa shugaban kasa zai zabo wani makusancinsa da suka dade da sanin juna."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel