Mutane 4 sun sake kamuwa da coronavirus a Kano, sun zama 77 a jahar

Mutane 4 sun sake kamuwa da coronavirus a Kano, sun zama 77 a jahar

Ma'aikatar lafiya ta Jahar Kano ta bayyana cewa an samu karin wasu mutane hudu da suka kamu da cutar coronavirus, inda hakan ya kawo jumillar adadin wadanda suka kamu zuwa 77 a jahar.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, ma'aikatar lafiyar ta ce ya zuwa ranar Lahadi, 26 ga watan Afrilu, mutane 77 ne suka kamu da cutar COVID-19, mutum daya ya mutu a cikinsu.

Tun a ranar Laraba ne rahotanni suka bayyana cewa an rufe dakin gwajin cutar coronavirus da ke Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke birnin Kano.

Sai da aka yi kwana biyu a jere hukumar NCDC ba ta bayar da rahoton sabbin mutanen da suka kamu ba daga Kano.

Dr Sani Aliyu, babban jami'i a kwamitin gwamnatin tarayya da ke yaki da yaduwar corona, ya ce an rufe cibiyar gwajin ne bayan wasu ma'aikatan lafiya sun harbu da cutar.

Tuni gwamnatin ta ce ta tura tawaga ta musamman zuwa Kano domin farfado da ayyuka a cibiyar.

KU KARANTA KUMA: Yawan mace-mace: Na damu da halin da Kano ke ciki – Hadimin Buhari ya roki yan Najeriya da su yi wa birnin addu’a

A halin da ake ciki, mun ji cewa gwamnatin Kano a karkashin Abdullahi Umar Ganduje ta ce ta kammala shirin kafa wasu kotu na musamman a wurare daban-daban domin hukunta masu sabawa doka.

Mai girma Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin cewa jama’a su zauna a cikin gidajensu a jihar Kano.

Sai dai ana samun wadanda su ke yi wa dokar hukuma kunnen kashi a jihar.

Wannan ya sa gwamna Abdullahi Ganduje ya shaidawa jihar Kano a lokacin da ya zanta da ‘yan jarida cewa za a rika hukunta masu sabawa dokar kullen domin a kare lafiyar Bayin Allah.

Gwamnan ya bayyana cewa batun rufe iyakokin jihar da aka yi ya na nan. Ganduje ya ce gwamnonin Arewa sun yarda su rufe iyakokinsu na makonni biyu a hana yaduwar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng