An sallami dukkan wadanda cutar covid-19 ta harba a garin da annobar ta samo asali a China

An sallami dukkan wadanda cutar covid-19 ta harba a garin da annobar ta samo asali a China

Yanzu haka babu sauran mai dauke da kwayar cutar covid-19 a birnin Wuhan na kasar China, inda annobar cutar covid-19 ta samo asali.

A ranar Lahadi ne wani babban jami'i a hukumar lafiya ta birnin Wuhan ya tabbatar da cewa babu sauran wani mai kwayar cutar coronavirus a asibitocinsu, duk sun warke kuma an sallamesu.

"Babban labarinmu a wannan rana, 26 ga watan Afrilu, shine babu sauran wani mai dauke da kwayar cutar covid-19 a birnin Wuhan. Mu na godiya ga kokarin Wuhan da ma'aikatan lafiya daga fadin kasa" a cewar Mi Feng, kwamishinan lafiya.

Rahotanni sun bayyana cewa mutane 46,452 ne aka tabbatar annobar covid-19 ta harba a Wuhan. Mutane 3,869 daga cikinsu sun mutu.

A sanarwar da China ta fitar ranar Lahadi, ta bayyana cewa an tabbatar da samun mutane goma sha daya kacal da annobar cutar covid-19 ta harba a fadin kasar.

An sallami dukkan wadanda cutar covid-19 ta harba a garin da annobar ta samo asali a China

An sallami dukkan wadanda cutar covid-19 ta harba a garin da annobar ta samo asali a China
Source: Twitter

Kazalika, sanarwar ta bayyana cewa an shiga rana ta goma sha daya ba tare da samun mutuwar mai dauke da kwayar cutar covid-19 ba a kasar China.

DUBA WANNAN: Mahaifiyar Ado Gwanja da sauran fitattun mutane 15 da suka mutu a cikin sa'o'i 24 a Kano

Biyar daga cikin sabbin mutanen da annobar cutar ta harba sun fito ne daga yankin Heilongjian mai makwabtaka da kasar Rasha.

An samu mutum guda daya da annobar ta harba a yankin Guangdong mai yawan masana'antu, wanda kuma ya yi iyaka da birnin Hong Kong daga kudu.

Sauran biyar din da aka samu sun shigo kasar ne daga ketare. China ta gano jimillar mutane 1,634 da suka shigo da cutar covid-19 cikin kasar daga ketare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel