Gwamnatin Anambra ta takaita dokar zaman gida a cikin gari - Obiano

Gwamnatin Anambra ta takaita dokar zaman gida a cikin gari - Obiano

Mun samu labari daga jaridar Daily Trust cewa gwamnatin jihar Anambra ta cire takunkumin da ta garkamawa mutanen jihar. Gwamnatin ta fitar da wasu dokoki da jama’a za su bi.

Gwamna Willie Obiano ne ya bada wannan sanarwa na takaita dokar zaman gida a lokacin da ya yi magana da mutanen jihar Anambra a jiya ranar Asabar, 25 ga watan Afrilu, 2020.

Wannan sassauci da gwamnan ya yi bai shafi masu shigowa cikin jihar ba. Sabuwar dokar za ta rika aiki ne kawai a cikin jihar, inda za a bar mutanen gari su shiga inda su ke bukata.

Har gobe gwamnatin jihar Anambra ba ta bude iyakokinta domin mutanen waje su shigo ba. Haka zalika gwamnan ya sanar da cewa dole mutane su rika amfani da tsummar rufe fuska.

Mai girma gwamnan ya tabbatar cewa zai tsawata sosai wajen ganin an bi wannan doka. Willie Obiano ya ce ba zai bari kowa ya tsallaka iyakar Anambara ya shigo masa cikin jiha ba.

KU KARANTA: NLC ta fadawa Shugaban kasa Buhari ya takaita takunkumin kulle

Gwamnatin Anambra ta takaita dokar zaman gida a cikin gari - Obiano

Mutane za su fara yawo a Anambra tare da tsummar kariyar fuska
Source: UGC

“An bude zirga-ziraga a cikin jihar Anambra. Dokar amfani da tsummar fusa ta fara aiki babu kama hannun yaro. Ka da wanda ya sake ya fita daga gidansa ba da tsummar fuska ba.”

Willie Obiano ya kuma bada sanarwar cewa masu saida abinci za su iya bude kasuwanninsu. Haka zalika gwamnatin jihar ta bada dama ga masu gidajen giya su bude shaguna yanzu.

Kwanakin baya dai gwamnatin Anambra ta rufe kowace kasuwa ta bukaci kowa ya koma gidansa ya zauna. An dauki wannan mataki ne domin hana yaduwar cutar COVID-19 a jihar.

Makonni biyu da su ka wuce ne aka fara samun wanda ya kamu da COVID-19 a jihar. Daga lokacin har zuwa yanzu babu labarin wanda aka sake samu ya na dauke da wannan muguwar cuta.

Obiano ya kuma yi kira ga jama’a su rika bin doka ta hanyar kaurcewa cinkoson jama’a da kuma yawan wanke hannuwansu da mai da kuma sabulu a bakin shiga kasuwannin da ke jihar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel