Dakunan ajiye gawa a asibitocinmu sun cika - Gwamnan Legas

Dakunan ajiye gawa a asibitocinmu sun cika - Gwamnan Legas

Babajide Sanwo-Olu, gwamnan Legas ya bayyana cewa dakunan ajiye gawa da ke asibitocin jihar sun cika makil.

A cewar gwamnan, akwai bukatar a rage yawan gawarwakin mutane da aka ajiye a dakunan ajiyar domin samun wurin da za a ajiye sabbin gawarwakin mutanen da suka mutu a jihar.

Gwamnan ya ce ba yana magana a kan mutanen da annobar cutar covid-19 ta kashe bane a jihar.

Ya ce gawarwakin na mutanen da suka mutu ne amma ba a samu damar binnesu ba saboda dokar kulle da aka saka

A saboda haka, Sanwo-Olu ya ce gwamnatinsa ta bawa wadanda za su binne gawar 'yan uwansu izinin zuwa asibitoci domin daukar gawarwakinsu tare da binnesu.

Dakunan ajiye gawa a asibitocinmu sun cika - Gwamnan Legas

Gwamnan Legas; Babajide Sanwo-Olu
Source: Twitter

Amma, ya ce akwai sharuddan da dole sai an cikasu lokacin da za a binne gawar mamaci. Sharuddan sune kamar haka;

1. Yawan mutane; 'yan uwa da malaman addini, da zasu raka gawa zuwa makabarta kar ya wuce 20

2. Tilas sai an yi biyayya ga tsarin nesanta da juna yayin binne gawar

DUBA WANNAN: Jerin sunayen fitattun mutane 16 da suka mutu a cikin sa'o'i 24 a Kano

3. Dole duk masu rakiyar gawar zuwa makabarta su saka safar hannu da takunkumin fuska, sannan kuma su wanke hannayensu da sabulu da zarar sun dawo gida.

4. Ba za a yi wani biki ba ko kadan kafin ko kuma bayan an dawo daga rakiyar gawa zuwa makabarta.

Sanwo-Olu ya jadda cewa ya zuwa yanzu mutane 20 ne suka mutu a jihar Legas bayan sun kamu da annobar cutar covid-19.

A saboda haka ya yi kira ga jama'a da su kwantar da hankalinsu, ba mutanen da annobar covid-19 ta kashe ya ke magana a kansu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel