Covid-19: Yara biyu sun mutu a dandazon jama'a yayin siyayyar azumin Ramadan

Covid-19: Yara biyu sun mutu a dandazon jama'a yayin siyayyar azumin Ramadan

- Yara biyu ne suka rasa rayuwarsu sakamakon cunkoso da dandazon jama'ar da aka samu a kasuwar Jalingo a jihar Taraba

- Hakan ya faru ne bayan gwamnatin jihar ta sasauta dokar hana zirga-zirga a jihar na sa'o'i hudu don su yi siyayyar azumi

- Iyayen yaran da suka rasu sun fadi ne a kasuwa dauke da goyonsu amma an garzaya da su asibiti inda yaran da ke bayansu suka ce ga garinku

Yara biyu ne suka rasu sakamakon dandazon jama'a da suka cika kasuwar Jalingo don siyayya.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, jama'ar sun fara turereniya da gaggawar zuwa kasuwa ne bayan an ba su sa'o'i kadan don siyayya.

Gwamnatin jihar ta bada daga karfe 10 na safe zuwa karfe 2 na rana don su yi siyayyar abubuwan bukata.

Dubban masu siyayya ne suka cika kasuwar don siyan kayan abinci, lamarin da ya jawo taruwar dandazon jama'a a kasuwar.

Dukkan yaran biyu da suka rasu suna goye ne a bayan iyayensu mata a lokacin da iyayen suka fadi tare da suma.

Covid-19: Yara 2 sun mutu a kasuwar Taraba bayan an sake su siyayyar azumi
Covid-19: Yara 2 sun mutu a kasuwar Taraba bayan an sake su siyayyar azumi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Jerin kasashen Afirka da suka fi yawan masu cutar Korona – WHO

An gaggauta garzayawa da su asibiti don samun taimakon masana kiwon lafiya.

Har a lokacin da aka rubuta wannan rahoton, ba a riga an gano sunayen iyayen yaran ba.

Wani ganau ba jiyau ba a kasuwar mai suna Hassan Zubairu ya ce masu yankar aljihu sun yi amfani da wannan cunkoson wajen yashe jama'a.

"Wata mata mai matsakaicin shekaru ta fasa ihu bayan ta gano cewa an kwashe mata dukkan kudin da ke jakarta," ganau din yace.

A lokacin da aka tuntubi kakakin hukumar 'yan sandan jihar, DSP David Misal ya ce 'yan sanda basu samu wannan rahoton ba.

A wani labari na daban, Kasuwannin jihar Kano sun yi matukar cika a ranar Alhamis bayan gwamnatin jihar ta sassauta dokar hana zirga-zirga da ta kafa a jihar don jama'a su shiryawa azumin watan Ramadan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164