Yanzu-yanzu: Cutar Korona ta sake kashe rai a Legas

Yanzu-yanzu: Cutar Korona ta sake kashe rai a Legas

- A yau gwamnatin jihar Legas ta sanar da karin mutuwar majinyaci daya sakamakon muguwar cutar Covid-19 a jihar

- Kamar yadda gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na twitter, wannan mutuwar ce ta kai jimillar wadanda suka ransu sakamakon cutar a jihar zuwa 19

- A jiya ne cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa ta NCDC ta sanar da cewa an samu karuwar mutum 114 a Najeriya masu cutar

A yau ne gwamnatin jihar Legas ta sanar da rasuwar wani majinyacin cutar Korona a jihar. Hakan ya kai jimillar mace-mace sakamakon cutar a jihar zuwa 19.

Ma'aikatar lafiya ta jihar ta bayyana hakan a shafinta na Twitter a ranar Asabar, sa'o'i kadan bayan an tabbatar da kamuwar mutum 80 da cutar a jihar.

Cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa ta NCDC ta sanar da cewa an sake samun karuwar 114 da suka kamu da cutar a kasar nan, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Daga cikin mutum 114 da suka sake kamuwa, akwai mutum 80 daga jihar Legas, 21 a Gombe sai babban birnin tarayya na da biyar.

Yanzu-yanzu: Cutar Korona ta sake kashe rai a Legas
Yanzu-yanzu: Cutar Korona ta sake kashe rai a Legas
Asali: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: A karo na farko, an samu bullar Korona a Zamfara

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya tabbatar da cewa mutane biyu sun kamu da kwayar cutar COVID-19 a jihar kamar yadda premium Times ta ruwaito.

Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin jihar ke sanar da cewa ta siya naurar ventilator 12 da kayan gwajin cutar 20,000 da za a ajiye a sansanin killace masu cutar a cewar kakakin gwamnan, Zailani Bappa.

A sakon da gwamnan ya fitar cikin dare a faifan bidiyo, ya ce gwajin da hukumar NCDC ta yi wa wasu mutane a jihar ya nuna mutum biyu sun kamu da cutar.

Gwamnan ya ce sakamakon gwajin ya nuna cewa gwamnatinsa ba azarbabi ta yi ba wurin daukan dokoki na kare yaduwar cutar a jihar tun kafin a gano bullar ta a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164