Yanzu-yanzu: Sabbin Mutane 114 sun kamu da Coronavirus, 21 a Gombe

Yanzu-yanzu: Sabbin Mutane 114 sun kamu da Coronavirus, 21 a Gombe

Cibiyar hana yaduwar cututtuka a Najeriya watau NCDC ta sanar da samun karin mutane 114 da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Juma'a, 24 ga Afrilu, 2020.

Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: “An samu karin mutane dari da sha hudu(17) sun kamu da #COVID19"

80 a Lagos

21 a Gombe

5 a FCT

2 a Zamfara

2 a Edo

1 a Ogun

1 a Oyo

1 a Kaduna

1 a Sokoto

A daidai karfe 11:30 na 24 ga Afrilu, an tabbatar kamuwar mutane 1095 da cutar COVID-19 a Najeriya

An sallmi: 208

Mutuwa: 32

Kawo yanzu, ga jerin jihohin da cutar ta bulla da adadinsu:

Lagos-657

FCT-138

Kano-73

Ogun-35

Gombe-30

Katsina-21

Osun-20

Edo-19

Oyo-18

Borno-12

Kwara-11

Akwa Ibom-11

Kaduna-10

Bauchi-8

Delta-6

Ekiti-4

Ondo-3

Rivers-3

Jigawa-2

Enugu-2

Niger-2

Abia-2

Zamfara-2

Sokoto-2

Benue-1

Anambra-1

Adamawa-1

Plateau-1

A bangare guda, Gwamnatin jihar Borno ta bukaci dakatar da wasu limamai uku na jihar a kan yin karantsaye ga dokar hana zirga-zirga ta jihar.

Mataimakin gwamnan jihar, Umar Kadafur ne ya sanar da hakan yayin tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Maiduguri a ranar Juma'a.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta wallafa, sun tattauna ne yayin da yake duban yadda jama'a suke bin dokar hana zirga-zirgar da gwamnatin ta saka a jihar.

"Limaman da suka karya dokar sun hada da Goni Isa na Flatari ta Arewa, Goni Bashir na CMC da kuma Goni Gabchiya, babban limamin jami'ar Maiduguri.

"Sun san da dokar hana zirga-zirgar amma sun ja sallar Juma'a, lamarin da ya taka umarnin gwamnatin jihar na kokarin hana yaduwar cutar Covid-19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel