Covid-19: Kura-kurai 7 da 'yan Najeriya ke tafkawa wajen amfani da takunkumi

Covid-19: Kura-kurai 7 da 'yan Najeriya ke tafkawa wajen amfani da takunkumi

Takunkumi ya zama wani bangare na suturar jama'ar Najeriya tun bayan bullar annobar cutar covid-19.

Hukumar shawo kan cututtuka ma su yaduwa ta kasa (NCDC) ta shawarci 'yan Najeriya su ke saka takunkumin fuska duk lokacin da su ka san za su kasance a cikin jama'a da yawa.

Hakazalika, wasu gwamnoni sun bawa jami'ai izinin tilastawa jama'a amfani da takunkumi yayin da za su fita daga gidajensu.

Masana da kwararru da dama sun yi bayani tare da bayar da shawara ga jama'a a kan yadda za su yi amfani tare da sarrafa takunkumin da su ka kammala amfani da su.

Sun bayyana hakan ne bayan sun lura cewa jama'a a Najeriya na yin wasu kura - kurai wajen yadda su ke amfani tare da sarrafa takunkumi.

1. Wasu daga cikin jama'a su na amfani da wasu takunkumi na musamman da ake amfani da su yayin tiyata a asibiti. Irin wadannan takunkumi ba na amfanin gama - garin jama'a ba ne.

2. Irin takunkumin da aka ambata a sama ba sa hana kwayoyin cuta fita yayin da mutum ke fitar da numfashi.

Mai dauke da kwayar cutar covid-19, wanda bai san ya na da ita ba, zai iya yadata zuwa wasu mutane duk da yana amfani da irin wadannan takunkumi.

Manyan jami'an gwamnati da ma su kudi ne su ka amfani da irin wadannan takunkumi.

DUBA WANNAN: Covid-19: Gwamnan PDP ya bayar da umarnin yin bulala ga duk wanda aka gani babu takunkumi a jiharsa

3. 'Yan Najeriya, da su ka hada da jami'an gwamnati, su na da al'adar sakale takunkumi a kasan habarsu, ba tare da rufe baki da hancinsu ba.

Ma su irin wannan dabi'a su na cikin hatsarin harbuwa da kwayar cutar covid-19 daga wurin ma su dauke da ita, musamman idan su ka sake mayar da takunkumin da suka sakale a haba bayan mu'amala da mai cutar.

4. Masana sun kula cewa 'yan Najeriya na yawan taba takunkumin fuskarsu da sunan gyara ma sa zama ko kuma yayin taba fuskarsu; ga ma su irin dabi'ar.

Kwayoyin cuta da ke jikin hannu za su iya makalewa a jikin takunkumi ko kuma mutum ya taba kwayoyin cutar da su ka makale a jikin takunkumin, wanda karshe zai iya harbuwa ko ya harbi wani da ita.

5. An lura cewa wasu su kan cire takunkumin fuskarsu ba tare da tsaftace hannunsu ba kafin yin hakan.

Wasu kuma kan saka takunkumin a cikin aljihunsu bayan sun cire shi, inda zai taba sauran abubuwan da mutum ya ajiye a aljihunsa daga nan kuma kwayoyin cuta su yadu.

Yin hakan zai haddasa yaduwar kwayoyin cuta zuwa sauran wasu abubuwa da mutum zai taba da hannunsa, daga nan kuma zai iya harbuwa ko kuma ya yada ta zuwa wasu.

6. Wasu kuma daukan lokaci mai tsawo su ke yi sanye da takunkumi guda a fuskarsu. Wasu ma har sake amfani da takunkumi su ke yi bayan sun cire shi a baya.

Ba a son takunkumi ya dauki lokaci mai tsawo ba tare da sauya shi ba.

Sake amfani da takunkumi zai iya haddasa yaduwar kwayoyin cuta da a farko takunkumin ya taresu.

7. Kuskure ne mutum ya cire takunkumi ya jefar saboda ya gama amfani da shi. Yin hakan kan iya zama sanadin yaduwar kwayoyin cututtuka.

An ja hankalin 'yan Najeriya a kan su bi shawarwarin da NCDC ta bayar a kan sarrafa takunkumin da aka gama amfani da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel