Covid-19: Gwamnatin Borno za ta dakatar da wasu limamai uku na jihar

Covid-19: Gwamnatin Borno za ta dakatar da wasu limamai uku na jihar

Gwamnatin jihar Borno ta bukaci dakatar da wasu limamai uku na jihar a kan yin karantsaye ga dokar hana zirga-zirga ta jihar.

Mataimakin gwamnan jihar, Umar Kadafur ne ya sanar da hakan yayin tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Maiduguri a ranar Juma'a.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta wallafa, sun tattauna ne yayin da yake duban yadda jama'a suke bin dokar hana zirga-zirgar da gwamnatin ta saka a jihar.

"Limaman da suka karya dokar sun hada da Goni Isa na Flatari ta Arewa, Goni Bashir na CMC da kuma Goni Gabchiya, babban limamin jami'ar Maiduguri.

"Sun san da dokar hana zirga-zirgar amma sun ja sallar Juma'a, lamarin da ya taka umarnin gwamnatin jihar na kokarin hana yaduwar cutar Covid-19.

"Abun yana da matukar bada haushi ta yadda jama'a ke daukar annobar Covid-19. Hakan ya bayyana ne ta yadda suka dauka dokar hana zirga-zirgar.

"Za mu tura sunayensu gaban Shehun Borno, Alhaji Umar Ibn Garbai, wanda shine shugaban sarakunan gargajiya na jihar Borno. Za a umarci babban limamin jihar da ya dakatar da su," yace.

Ya ce kwamitin yaki da yaduwar cutar za ta tabbatar da an bi dokar. Za ta kama tare da killace duk matafiya wandanda ke yunkurin shiga garin ta hanyoyi daban-daban.

Covid-19: Gwamnatin Borno za ta dakatar da wasu limamai uku na jihar
Covid-19: Gwamnatin Borno za ta dakatar da wasu limamai uku na jihar
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Covid-19: Ganduje ya aika wa masu dakunan gwaji na jihar da sakon gaggawa

A cewarsa, "Kwamitin ya lura cewa duk da dokar da aka saka da kuma rufe hanyoyin shiga jihar, ana shiga jihar ta hanyar Damaturu zuwa Gaidam ta Bosso.

"Akwai hanyar Gombe zuwa Biu da kuma Damboa zuwa Maiduguri da mutane ke bi. Wasu kuma na bi ta Madagali zuwa Gwoza da kuma Bama zuwa Maiduguri."

Kadafur ya ce gwamnatin za ta fara bibiyar jama'a masu karya doka tare da kama su.

"Gwamnatin ba za ta lamunci karya doka ba yayin da jihar ke kulle. Hakan ne kadai zai iya jaddada shawo kan barkewar annobar a jihar," yace.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, Babban limamin jihar Borno, Laisu Ibrahim, ya ja kunnen limaman a kan jan jam'in sallar Juma'a da na sallolin farilla biyar na kowacce rana a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel