Da duminsa: Allah ya yiwa sarkin Malaman Sokoto rasuwa

Da duminsa: Allah ya yiwa sarkin Malaman Sokoto rasuwa

Inna liLLahi wa inna ilaihi raji'un! Allah ya yiwa sarkin Malaman daular Usmaniyyar, Sheikh Buhari Sirdawa, rasuwa.

Ya rasu ne da yammacin Juma'a a asibitin Saraki bayan gajeruwar rashin lafiya da yayi.

Tsohon sarkin Musulmai, Sultan Abubakar III ya nada marigayin Sarkin Malamai ne shekaru 45 da suka wuce.

Ya rasu yana mai shekaru 95 kuma ya bar 'yaya 34; mata 20 da maza 14. Hakazalika jikoki da dama da tattaba kunne.

A cewar daya daga cikin yaransa, Yahaya Buhari, ya ce za'a yi Sallar Jana'iza a Masallacin Shehu.

Ya bayyanawa Daily Trust cewa marigayin ya rubuta cikin wasiyyarsa cewa a birneshi gefen kabarin iyayensa dake gidansa, duk da cewa Sarkin Musulmi ya ce a birneshi a Hubbaren Shehu.

Yaron yace: "Zamu bayyanawa Sultan abinda ke cikin wasiyyarsa kuma mun sa zai amince da hakan."

Da duminsa: Allah ya yiwa sarkin Malaman Sokoto rasuwa

Da duminsa: Allah ya yiwa sarkin Malaman Sokoto rasuwa
Source: Facebook

Mun kawo muku rahoton cewa an samu bullar cutar Coronavirus a Sakkwaton Shehu, Gwamnatin jihar ta tabbatar.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana hakan ne a jawabin da yayiwa manema labarai da daren Litinin, 20 ga watan Afrilu, 2020.

A cewarsa, mutumin d aya kamu na kwance a asibitin koyarwan jami'ar Usamnu DanFodio, dake jihar.

Yace: "Ya ku al'ummar jihar Sokoto, cikin bakin ciki nike mai sanar muku da labaran cewa an samu bullar annobar Coronavirus a nan jihar Sokoto."

"Tunda an tabbatar da kamuwa mutumin, za'a kai shi cibiyar killacewa dake Amanawa."

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya kafa kwamiti mai mambobi 32 wadda za su raba wa alumma abinci lokacin azumin watan Ramadan ta hanyar bin dokokin kiyaye yaduwar COVID-19.

Tambuwal ya ce sakataren gwamnatin jihar, Saidu Umar ne zai jagoranci kwamitin yayin da dan majalisar tarayya mai wakiltan Silame/Binji, Mani Maishinku zai kasance cikin mambobin.

Mambobin sun hada da Abubakar Shamaki, Abdullahi Maigwandu, Bello Aliyu, Abubakar Jibril, Malam Abubakar Mabera, Auwal Romo, Lawal Maidoki, Prof. Abubakar Yagawal, Bello Yabo da Yahaya Na Malam Boyi.

Akwai kuma Prof. Mansur Ibrahim, Malam Amadu Helele, Malam Nura Hausare, Dr Jabir Sani-Maihula, Malam Zaruku Masallacin Shehu, Malam Husaini Gandu, Ibrahim No Delay, Farouk Suyudi da Bello Guiwa.

Sauran mambobin su ne arkin Yakin Gagi, Ubandoman Sabon Birni, Sarkin Kudun Guiwa, Prof. Sadiya Bello, Malama Aishatu Salihu, Malama Zainab Binji, Hajiya Inno Attahiru da Hajiya Fati Illo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel