Covid-19: Jami'ar Tarayya ta Jigawa za ta fara gwajin ingancin maganin da ta hada

Covid-19: Jami'ar Tarayya ta Jigawa za ta fara gwajin ingancin maganin da ta hada

- Jami'ar gwamnatin tarayya ta jihar Jigawa da ke garin Dutse ta bayyana cewa za ta fara gwajin ingancin maganin cutar Covid-19 da ta hada

- Kamar yadda shugabar makarantar, Farfesa Fatima Batul Mukhtar ta ce cutar na shigowa kasar nan sashen bincike na jami'ar ya fara aikin hada magani

- Shugaban kungiyar masu binciken, Dr Salihu Ibrahim ya tabbatar da cewa sun fara hada maganin ne tare da hadin guiwar masu maganin gargajiya

Jami’ar gwamnatin tarayya da ke jihar Jigawa a garin Dutse ta ce ta fara gwajin ingancin maganin cutar Covid-19 wanda ta samo daga tsirrai.

Hukumar jami’ar ta sanar da hakan ne a ranar Juma’a a cikin takardar da ta fitar, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Shugabar makarantar, Farfesa Fatima Batul Mukhtar ta ce jami’ar ta gaggauta fara neman maganin cutar ne tun bayan barkewar annobar a Najeriya.

Hukumar jami’ar ta umarci sashin binciken ta da ya samo magani amma wanda ake iya samu a gida Najeriya don yakar cutar.

Covid-19: Jami'ar tarayya ta Jigawa za ta fara gwajin ingancin maganin da ta hada

Covid-19: Jami'ar tarayya ta Jigawa za ta fara gwajin ingancin maganin da ta hada
Source: UGC

DUBA WANNAN: Covid-19: Ganduje ya aika wa masu dakunan gwaji na jihar da sakon gaggawa

Shugaban kungiyar masu binciken, Salihu Ibrahim, ya ce jami’ar ta hada guiwa da masu maganin gargajiya ne don gano magungunan da ake amfani dasu na gargajiya wajen shawo kan zazzabi mai zafi, tari da kuma cutar lamoniya.

Kamar yadda yace, kungiyarsa ta yi kokari wajen ganowa, tantancewa tare da tatso magungunan daga tsirrai.

Dr Salihu ya ce ana gwada maganin a kan dabbobi don gano ko yana illa. A halin yanzu ana gwajin a jikin dabbobin ne na kwanaki 28 amma ba a kammala ba.

Shugaban kungiyar binciken ya ce za a fara gwajin ingancin maganin a kan mutane ne daga ranar 14 ga watan Mayu zuwa 14 ga watan Yunin 2020.

Za a gwada maganin a kan masu jinyar cutar lamoniya ne daga ranar 14 ga watan Yuni zuwa 14 ga watan Yulin 2020.

Tun bayan shigowar annobar Covid-19 kasar Najeriya, ta ci gaba da yaduwa cikin jihohin kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel