Jihohi 27 da aka samu bullar cutar Covid-19 a Najeriya - NCDC
Babu shakka hukumomin lafiya na ci gaba da aiki tukuru domin dakile yaduwar cutar coronavirus a Najeriya, sai dai fa lamarin ya ci tura domin kuwa cutar na ci gaba da bazuwa a kasar.
A halin yanzu an samu bullar cutar covid-19 a jihohi 27 na Najeriya ciki har da babban birnin tarayya kamar yadda alkaluman cibiyar dakile yaduwar cututtuka a kasar NCDC suka tabbatar.
Taskar bayanai ta NCDC a ranar Alhamis, 23 ga watan Afrilun 2020, ta ce cutar corona ta harbi mutane 981 yayin da mutum 197 suka samu waraka.
Ya zuwa yanzu dai mutane 31 cutar ta hallaka a fadin Najeriya kamar yadda bayanan alkaluman NCDC suka tabbatar.
Ga jerin adadin mutanen da suka kamu da cutar a kowace daya daga cikin jihohi 25 na Najeriya da cutar ta bulla:
Lagos-582; FCT-133; Kano-73; Ogun-29; Katsina-21; Osun-20; Oyo-17; Edo-17; Borno-12; Kwara-11; Akwa Ibom-11; Kaduna-9; Gombe-9; Bauchi-8; Delta-6; Ekiti-4; Ondo-3; Rivers-3; Jigawa-2; Enugu-2; Niger-2; Abia-2; Benue-1; Anambra-1; Sokoto-1; Adamawa-1; Plateau-1.
Da misalin karfe 11.30 na daren ranar Alhamis, NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane 108 da cutar covid-19 ta harba a fadin Najeriya.
Jihohin da cutar ta bulla karo na farko a baya-bayan nan sun kasance Adamawa a yankin Arewa maso Gabas da kuma jihar Filato a yankin Arewa ta Tsakiya.
Har ila yau jihar Legas ce a kan sahu na gaba ta fuskar yawan wadanda cutar ta harba, sai kuma birnin Abuja a mataki na biyu yayin da jihar Kano ta biyo bayansu.
KARANTA KUMA: Rundunar Sojin saman Najeriya ta kara inganta ayyukan gudanarwa na dakarunta
Taswirar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta tabbatar cewa mutane 2,729,274 cutar ta harba a fadin duniya inda jimillar wadanda suka mutu kuma ta kai 191,614.
A Larabar makon nan da muke ciki, mun ji cewa an dakatar da gwajin gano wadanda cutar corona ta harba a jihar Kano sanadiyar rashin kayan aiki na aiwatar da gwajin.
Farfesa Sadiq Isah na kwamitin yaki da cutar corona a Kano, shi ne ya bayar da shaidar hakan da cewa dole ce ta sanya aka dakatar da gwajin don babu sinadaran da ake bukata domin ci gaba da gwajin.
Daga bisani kuma Farfesan ya shaidawa sashen Hausa na BBC cewa, an kai sinadaran gwaje-gwajen amma babu damar ci gaba da aiki a dakin gwajin har sai bayan kwanaki biyu.
Dalilin hakan kuwa shi ne an riga da yin feshin kashe kwayoyin cuta a dakin da sai bayan an dauki wani tsawon lokaci kana a shige sa.
Sanadiyar rashin ci gaba da gwaje-gwajen a birnin Kano, ya sanya kwanaki biyu a jere mahukuntan lafiya a jihar ba su fitar da alkaluman wadanda cutar ta harba a Kanon ba.
Idan ba a manta ba a ranar 11 ga watan Afrilun 2020 ne ma'aikatar Lafiya a Kano ta sanar da bullar cutar karo na farko a jikin wani tsohon Kwamishinan jihar bayan dawowarsa daga Birtaniya.
Tun daga wannan lokaci dai likafar annobar ta ci gaba a sanadiyar yadda take yaduwa tamkar wutar daji.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng