Dubi wasu kasashe guda 15 a Duniya da ba’a samu bullar cutar COVID-19 ba
Yayin da gwamnatocin kasashen duniya ke cigaba da yaki da yaduwar annobar Coronavirus a kasashen su, akwai wasu kasashe guda 15 da har yanzu cutar ba ta ratsa su ba.
Daily Trust ta ruwaito tun daga lokacin da cutar ta bulla a kasar China a watan Disambar 2019, ta kama mutane fiye da miliyan 2.6, daga ciki mutane 185,504 sun mutu, 730,843 sun warke.
KU KARANTA: An sake samun bullar Coronavirus a Katsina, Masari ya garkame karamar hukumar Safana
Amma cikin ikon Allah, kasashe biyu daga cikin kasashen nahiyar Afirka 54 basu samu bullar annobar nan a cikinsu ba, wadannan kasashen Afirka su ne Lesotho da Comoros.
Kasar Lesotho na da kimanin jama’a 2,139,031, Lesotho ta yi iyaka da kasar Afirka ta kudu, wanda take da mutane 3,635 dake dauke da cutar, amma duk da haka cutar bata shige ta ba.
Yayin da Comoros ke da jama’a 865,950, sai dai tana kan tsibiri ne a tsakiyar ruwa, don haka ake ganin kasancewar bata da makwabciya, tana tsakiyar ruwa shi yasa babu cutar a kasar.
Sauran kasashen sune: Kiribati, Marshall Islands, Federated States of Micronesia, Nauru, Palau Samoa, Solomon Islands, Tajikistan, Tonga, Turkmenistan, Tuvalu, Vanuatu da Koriya ta Arewa.
A Najeriya kuwa, an samu sabbin mutane 108 da suka kamu da cutar Coronavirus kamar yadda hukumar dakile yaduwar cututtuka, NCDC ta bayyana a daren Alhamis.
NCDC ta ce sakamakon karin masu cutar a Najeriya, jimillan masu cutar ta hau zuwa 981, inda mutane 31 suka mutu, yayin da wasu 197 suka warke.
A wani labari kuma, Gwamnan Bauchi, Bala Muhammad ya sanar da garkame wuraren bauta, wuraren taron jama’a da kasuwanni a kokarinsa na dakile yaduwar cutar Coronavirus.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake ma al’ummar jahar jawabi a ranar Alhamis, inda yace ya dauki matakin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki.
Ya ce sun tattauna matsalar yaduwar cutar a jahar Bauchi, da sauran matsalolin kiwon lafiya a suka dabaibaye al’ummar jahar. A yanzu akwai mutane 8 dake dauke da cutar a jahar.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng