Ba za mu lamunci cin zarafin 'yan Najeriya a China ba - FG

Ba za mu lamunci cin zarafin 'yan Najeriya a China ba - FG

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta tabbatar wa da kasar China cewa ba za ta lamunci wariya ko nuna hantarar banbancin launin jinsi ba daga kasarsu.

A makonni uku da suka gabata, an samu rahotanni da ke bayyana cewa jami'an tsaron kasar China suna hantarar 'yan Najeriya da sauran 'yan kasashen Afrika, gidan talabijin din Channels ta ruwaito.

A yayin jawabi ga kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar coronavirus a ranar Alhamis, Geoffrey Onyeama, ministan harkomin waje, ya ce gwamnatin Najeriya za ta tattauna da sauran kasashen Afrika don samun mafita.

"A halin yanzu muna tattaunawa da gwamnatin kasar China din a kowanne mataki na gwamnatin Guangzhou da Beijing," yace.

"Mun sanar da gwamnatin kasar China cewa ba za mu lamunci cin zarafi da nuna banbancin launin fata ga 'yan Najeriya ko bakake ba daga garesu.

Ba za mu lamunci cin zarafin 'yan Najeriya a China ba - FG
Ba za mu lamunci cin zarafin 'yan Najeriya a China ba - FG
Asali: Twitter

KU KARANTA: Covid-19: Buhari ya halarci taron ECOWAS ta yanar gizo (Hotuna)

"Sun sanar da mu cewa babu wani abinda yake faruwa a hukumance amma kuma muna ganin bidiyo suna yawo. Na samu rahotanni ba kadan ba a kan hakan.

"Wannan ba zai yuwu ba kuma za mu tattauna da sauran kasashen Afrika don sanin matakin da za mu dauka a kan al'amarin." Cewar Onyeama

Ministan ya ce ya umarci ofishin jakadancin Najeriya da ke Guangzhou da su bayyana duk wani cin zarafi da aka yi musu, nuna banbancin launin fata ko cin tozarci.

"Za mu bi diddigin komai da ya faru koda kuwa akwai bukatar biyan diyya ne zamu bibiyi gwamnatin kasar China din,"

"A bangarenmu, har sai mun ga abinda ya turewa buzu nadi. Abun ya matukar tunzura mu saboda muna da dangantaka mai karfi tsakaninmu da gwamnatin kasar.

"Ba mu taba tsammanin wannan lamarin zai fito daga bangaren China ba," yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel