Me ya yi zafi: Dan sanda ya harbe abokiyar aikinsa har lahira a Ribas

Me ya yi zafi: Dan sanda ya harbe abokiyar aikinsa har lahira a Ribas

Wata budurwar 'yar sanda mai suna Lovender Elekwachi mai aiki a Eneka, wacce ke kula da cunkoson shataletalen Eneka ta rasu bayan abokin aikinta ya harbeta.

Elekwachi mai matsayin sajan ta rasu ne a ranar Alhamis bayan Sajan Bitrus Osaiah ya harbeta da bindiga.

Gidan talabijin din Channels ya ruwaito cewa, rundunar 'yan sandan jihar Ribas ta damke Osaiah tare da mika shi sashen binciken manyan laifuka na rundunar.

Me ya yi zafi: Dan sanda ya harbe abokiyar aikinsa har lahira a Ribas
Me ya yi zafi: Dan sanda ya harbe abokiyar aikinsa har lahira a Ribas
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Kano: Ganduje ya kaddamar da rabon tallafin abinci ga mabukata (Hotuna)

An damke mambobi biyu daga cikin 'yan kwamitin don amsa tambayoyi.

Hakazalika, an kwace mota kirar Hilux wacce ke hannun kwamitin sannan an mika gawar sajan din zuwa ma'adanar gawawwaki.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Joseph G. Mukan, ya bukaci a yi bincike mai tsauri don bankado abinda ya kai ga mutuwar jami'ar.

Ya yi kira ga jama'a da su kwantar da hankulansu har zuwa lokacin da sakamakon bincike zai fito don aiwatar da adalcin da ya dace.

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci taron kungiyar hadin kan kasashen Afrika ta yamma a Abuja da aka yi a ranar Alhamis.

Taron an yi shi ne ta bidiyon hadi tsakaninsa da shugabannin kasashen Afrika ta yamma. Sun samu tattaunawa ne a kan illar annobar Coronavirus a yankin.

A yayin taron, shugabannin kungiyar hadin kan kasashen Afrika ta yamma sun nada shi a matsayin gwarzon yaki da cutar coronavirus a yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel