'Yan sanda sun damke matar da ta kashe mai aikinta a kan albashi

'Yan sanda sun damke matar da ta kashe mai aikinta a kan albashi

Sashen binciken manyan laifuka na 'yan sandan jihar Legas da ke Yaba ya damke wata mata mai suna Nene Steve a kan zarginta da ake da kashe mai aikinta mai suna joy Adole.

An zargi cewa ta yi wa hadimarta duka ne wanda ya yi ajalinta a kan albashinta. Lamarin ya faru ne a gida mai lamba 18 da ke titin Ogundola da ke yankin Bariga ta jihar Legas, jaridar Leadership ta ruwaito.

A yayin bayyana yadda lamarin ya faru, Philip Ejeh, wanda shine babban yayan mamaciyar, ya ce ya matukar shiga damuwa bayan da aka sanar da shi mutuwar 'yar uwarsa.

Ya bayyyana cewa, mamamciyar 'yar asalin jihar Benuwai ce kuma an kaita Legas ne inda ta fara aiki a gidan a watan Janairun 2020.

"Ta kai korafin cewa uwar dakinta bata ba ta albashinta kuma tana shan duka duk lokacin da ta tambayeta.

"Tana kokarin barin gidan ne amma ta kasa saboda dokar hana zirga-zirgar da aka saka. A ranar Lahadi ne uwar dakinta ta yi mata mugun dukan da ya kai ga ajalinta," Ejeh yace.

Ya ci gaba da cewa, "Uwar dakin Ejeh ta ce da kanta ta sagale kanta har ta mutu.

"Kanwata ta samu aikin nan ne saboda tana son ci gaba da karatunta amma bata da hali. A yanzu uwar dakinta ta kasheta saboda bata son biyanta albashinta.

'Yan sanda sun damke matar da ta kashe mai aikinta a kan albashi

'Yan sanda sun damke matar da ta kashe mai aikinta a kan albashi
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Covid-19: 'Yan sanda sun halaka wani mutum da ya yi yunkurin daukarsu bidiyo suna kwallo

"A halin yanzu da ake magana, mun kai rahoto fannin binciken manyan laifuka da ke Panti a Yaba. An adana gawarta a ma'adanar gawawwaki kuma za a bincike silar mutuwarta."

Ya yi kira ga gwamnatin jihar Legas da duk masu fadi a ji na kasar nan da su taimaka musu wajen tabbatar da an yi musu adalci.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, DSP Bala Elkana ya tabbatar da cewa matar da mijinta sun kai rahoton cewa mai aikinsu ta kashe kanta.

Jami'an 'yan sandan sun ziyarci gidan amma sun zargi cewa akwai lauje cikin nadi.

Daga kan yadda aka nada igiyar da ke wuyanta zuwa ciwukan da ta samu duk suna nuna cewa kashe yarinyar aka yi ba ita ta kashe kanta ba.

Ya ce, "Yan sanda suna bincike a halin yanzu kuma sun tabbatar da cewa akwai alamun cin zarafi a gawarta. An azabtar da ita sannan aka nada igiya a wuyanta."

Ya kara da cewa, 'yan sandan sun mika gawarta asibiti don tabbatar da abinda ya kasheta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel