Covid-19: Likitoci uku sun kamu da cutar Korona a jihar Legas

Covid-19: Likitoci uku sun kamu da cutar Korona a jihar Legas

- Kungiyar likitoci ta jihar Legas ta tabbatar da cewa likitoci uku ne na kungiyar suka kamu da cutar Covid-19 a jihar

- Kamar yadda shugaban kungiyar da sakataren kungiyar suka bayyana, an tabbatar da likitocin na dauke da cutar ne a yau Alhamis

- Shugabannin kungiyar sun shawarci likitocin jihar da su guji taba marasa lafiya ba tare da isassun kayan kariya ba gudun kamuwa da cutar

Kungiyar likitoci da ke aiki da jihar Legas ta bayyana cewa likitoci 3 ne na kungiyar suka kamu da cutar coronavirus a jihar, jaridar The Nation ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Dr Oluwajimi Sodipo da sakataren kungiyar, Dr Ismail Ajibonwo ne suka sanar da hakan a ranar Alhamis a shafin kungiyar na Instagram.

Sodipo da Ajibonwo sun ce likitocin uku suna cibiyar killacewa ta jihar da ke Legas don karbar magani.

Sun ce a halin yanzu dai rashin lafiyar likitocin bai tsananta ba kuma suna samun goyon baya daga kungiyar.

Shugabannin kungiyar sun shaida cewa likitocin na aiki ne babban asibitin Alimosho, asibitin Ikorodu da kuma asibitin koyarwa na jami'ar jihar Legas.

Covid-19: Likitoci uku sun kamu da cutar Korona a jihar Legas

Covid-19: Likitoci uku sun kamu da cutar Korona a jihar Legas
Source: UGC

DUBA WANNAN: Covid-19: Korona ta kashe mutum biyu a Borno da Ribas, mutum 6 sun sake kamuwa

"Tun bayan aukuwar lamarin, muna aiki da wakilanmu na cibiyoyi daban-daban da kuma shugabannin asibitoci don tabbatar da an gwada jama'a.

"Ana hakan ne don hana yaduwar cutar a jihar," yace.

Shugabannin kungiyar sun ce za su shawarci gwamnatin jihar da ke saka likitoci a sahun gaba wajen yakar cutar, da su samarwa likitocin kayan kariya da kyautatawa don gudun kamuwa da cutar.

Sun bayyana cewa gwamnatin jihar na matukar kokari wurin yaki da cutar.

Shugabannin kungiyar sun shawarci likitoci da su guji taba marasa lafiya kai tsaye ba tare da kayan kariya ba.

Kungiyar ta nuna godiyarta ga likitocin a kan irin kokarin da suke yi wajen yaki da cutar a jihar.

A wani labari na daban, a yau an sake samun mutuwar mutum 2 sakamakon cutar coronavirus a jihar Legas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel