Covid-19: Jihar Kaduna ta samu dakin gwaji, ta horar da ma'aikata 22,000

Covid-19: Jihar Kaduna ta samu dakin gwaji, ta horar da ma'aikata 22,000

- Sakamakon kokarin gwamnatin jihar Kaduna na ganin an samu damar gwada jama'a da yawa a jihar, ta bude dakin gwaji a babban birnin jihar

- Kwamishinan lafiya ta jihar, Dr Amina Baloni ta sanar da cewa dakin gwajin an samar da shi ne a wuri mai zaman kansa

- Ta kara da cewa za a kara wasu dakunan gwaji biyu; daya a asibitin Ahmadu Bello da ke Zaria sai dayan a asibitin Yusuf Dantsoho da ke babban birnin jihar

A kokarin ganin an samu damar gwada mutane masu yawa a kan cutar coronavirus, gwamnatin jihar Kaduna ta samar da dakin gwaji na cutar coronavirus na farko a babban birnin jihar, jaridar The Cable ta ruwaito.

Kwamishinan lafiya ta jihar, Dr Amina Baloni, wacce ta sanar da hakan ga manema labarai, ta ce an samar da cibiyar gwajin ne a wuri mai zaman kansa kuma an yi hakan ne don samun damar gwada jama'a masu yawa a jihar.

Ta bayyana cewa, nan ba da dadewa ba za a samar da wasu dakunan gwaji biyu a asibitin koyarwa na Ahmadu Bello da ke Zaria da kuma asibitin Yusuf Dantsoho da ke babban birnin jihar a Kaduna.

Hakan ne zai sa jimillar dakunan gwajin kwayar cutar a jihar ya kai uku.

Covid-19: Jihar Kaduna ta samu dakin gwaji, ta horar da ma'aikata 22,000
Covid-19: Jihar Kaduna ta samu dakin gwaji, ta horar da ma'aikata 22,000
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Covid-19: Korona ta kashe mutum biyu a Borno da Ribas, mutum 6 sun sake kamuwa

Ta kara da cewa, an kara samar da wata cibiyar killacewa a jihar wacce za ta dauka majinyata a kalla 150.

Baloni ta bayyana cewa, ma'aikatan lafiya 22,000 aka horar a jihar.

A wani bangare kuwa, ta ce an zargi mutane 115 na dauke da cutar kuma an zakulo 174 da suka yi mu'amala da masu cutar.

103 kuwa sun killace kansu na makonni biyu kuma sun fita lafiya.

A wani labari na daban, a ranar Laraba ne gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya ce ya warke daga muguwar cutar coronavirus bayan gwaji har kashi biyu sun nuna babu cutar a tare da shi.

El-Rufai a matsayin wanda ya yi nasarar samun lafiya, ya kwatanta cutar da babban kalubale ga jama'a. Ya ce ba zai yi wa babban makiyinsa fatan samun cutar ba, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

A jawabin kai tsaye da gwamnan ya yi ga jama'ar jihar, ya ce, "Ina matukar farin cikin sanar da ku cewa yau Laraba ta tabbata bana dauke da cutar coronavirus bayan gwaji na biyu da aka yi min."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel