Sojojin Najeriya sun murkushe wasu yan bindiga a Benuwe, sun lalata mafakarsu
Shelkwatar tsaro ta rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa Sojoji sun kai samame wani sansanin yan bindiga dake jahar Benuwe inda suka kashe kashe miyagu guda uku.
Shugaban sashin watsa labaru na shelkwatar, Manjo Janar John Enenche ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, inda yace Sojojin sun kai samamen ne a ranar Laraba, 22 ga watan Afrilu.
KU KARANTA: Ji ka karu: Menene adadin lokacin da kwayar cutar Coronavirus take dauka kafin ta mutu?
Enenche yace Sojojin sun cimma yan bindigan ne a sansaninsu dake Anku Mbagen, cikin mazabar Atera-Jange Torov na karamar hukumar Ukum, inda suka kwashe dimbim makamai.
Enenche ya ce Sojojin Operation Whirl Stroke ne suka kai samamen daga cibiyarsu dake Katsina, karamar hukumar Ukum da kuma shiyya ta 4 daga wasu yankunan jahar Taraba.
Ya kara da cewa harin ya biyo bayan samun bayanan sirri dake tabbatar da cewa yan bindiga suna zirga zirga a wanann yankin dake kan iyakar jahohin Benuwe da Taraba.
“Ko da suka hangi Sojojin, sai suka bude musu wuta, nan da nan Sojojin suka rama biki, inda suka kashe mutane uku daga cikinsu, yayin da sauran suka jefar da makamansu suka ranta ana kare dauke da raunukan harbi.
“Daga cikin makaman da muka samu akwai manyan bindigu guda 21 da suka hada da 81mm Mortar Gun 1, 60mm Mortar Gun 5, bindigu guda 9 hadin gida, SMG guda 3, bindigar G3 guda 2 da kuma bindiga mai baki biyu guda 3.
“Sauran sun hada da alburusai da dama, babura uku, wayar salula, layu da miyagun kwayoyi, batirin mota da kuma kakin Sojoji guda 9.
"Babu Soja 1 da ya samu rauni ko ya mutu, da wannan muke tabbatar ma yan Najeriya manufar mu na tabbatar da zaman lafiya a kasa.” Inji shi.
Daga karshe ya nemi jama’a su cigaba da shayar da rundunar Soji bayanan sirri masu sahihanci domin samun daman yaki da miyagu a duk inda suke a cikin kasar.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng