Sakamakon bincike: An bankado dabbar da ta yi sanadiyyar samuwar Coronavirus a duniya

Sakamakon bincike: An bankado dabbar da ta yi sanadiyyar samuwar Coronavirus a duniya

Majalisar dinkin duniya, UN, ta hannun hukumar kiwon lafiya ta duniya, WHO, ta sanar da cewa an samu cutar COVID19, wanda aka fi sani da suna Coronavirus ne daga jikin Jemage.

Jaridar RFI ta bayyana cewa WHO ta tabbatar da hakan ne bayan wani bincike da ta kaddamar don gano asalin cutar, inda sakamakon binciken ya nuna cewa daga jemage aka samo cutar.

KU KARANTA: Ji ka karu: Menene adadin lokacin da kwayar cutar Coronavirus take dauka kafin ta mutu?

A yanzu haka, wannan cuta mai toshe numfashin dan Adam ta kama mutane fiye da miliyan 2, kuma ta kashe mutum 160,000 a tsakanin kasashen duniya 170.

Shugaban WHO, Tedros Ghebreysus ne ya tabbatar da alkalumman yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Laraba, 23 ga watan Afrilu a birnin Geneva, kasar Switzerland.

“A duniya gaba daya, mutane miliyan 2.5 ne cutar COVID-19 ta kama, kuma an samu mace mace 160,000 a dalilin ta.” Inji shugaban WHO, Tedros Ghebreysus.

Sakamakon bincike: An bankado dabbar da ta yi sanadiyyar samuwar Coronavirus a duniya
Sakamakon bincike: An bankado dabbar da ta yi sanadiyyar samuwar Coronavirus a duniya
Asali: UGC

Game da asalin cutar Coronavirus kuwa, mai magana da yawun hukumar WHO, Fadela Chaib ta shaida cewa hujjojin da suka tattara sun nuna cewa, cutar ta samo asali ne daga Jemage.

Wannan sabon bincike da WHO ta gudanar zai kawo karshen cece kucen da ake ta yi tsakanin manyan kasashen duniya da kasar China, inda suke zargin China da kirkirar cutar da gangan.

Idan za’a tuna a watan Disambar 2019 aka samu bullar cutar na farko a duniya a birnin Wuhan dake kasar China, inda ta tafka mummunan barna a birnin, amma a yanzu an samu saukinta.

A wani labari kuma, Legit.ng ta kawo muku jerin wasu wuraren da kwayar cutar Coronavirus ta fi kwanciya da lokacin da take dauka kafin ta mutu, domin kauce mata.

- Takarda: Kwayar cutar Coronavirus na daukan tsawon sa’o’i 3 kafin ta mutu

- Kayan sawa: Kwayar cutar Coronavirus na daukan tsawon sa’o’i 24 kafin ta mutu

- Bango: Kwayar cutar Coronavirus na daukan tsawon sa’o’I 36 kafin ta mutu

- Wayan karfe: Kwayar cutar Coronavirus na daukan tsawon kwanaki 3 kafin ta mutu

- Takardar kudi: Kwayar cutar Coronavirus na daukan tsawon kwanaki 4 kafin ta mutu

- Kofin gilashi: Kwayar cutar Coronavirus na daukan tsawon kwanaki 4 kafin ta mutu

- Cokula da kwanukan silba da na roba: Kwayar cutar Coronavirus na daukan tsawon kwanaki 7 kafin ta mutu

- Kyallen rufe fuska: Kwayar cutar Coronavirus na daukan tsawon kwanaki 7 kafin ta mutu

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng