Ganduje ya sake sabunta nadin mukamin shugaban hukumar yaki da rashawa na Kano

Ganduje ya sake sabunta nadin mukamin shugaban hukumar yaki da rashawa na Kano

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya sake sabunta nadin mukamin Alhaji Muhuyi Magaji Rimingado, karo na biyu.

Ganduje ya sabunta nadin mukamin Alhaji Muhuyi a matsayin shugaban Hukumar karbar korafe-korafen jama'a da kuma yaki da rashawa ta jihar.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, sakataren yada labarai na fadar gwamnatin Kano, Malam Abba Anwar, shi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, 22 ga Afrilu, 2020.

A cewar Malam Anwar, mukamin Alhaji Rimingado a wa'adi na biyu na tsawon shekaru biyar zai fara aiki ne daga watan Mayu na gobe daidai lokacin da wa'adinsa na farko zai karkare.

Malam Anwar ya ruwaito Ganduje yana cewa, "A yayin da wa'adin kujerar zai kare a watan gobe, dokokin da hukumar ta tanada sun bayar da dama a tsawaita wa'adin shugabanta."

Gwamnan Kano; Abdullahi Ganduje
Gwamnan Kano; Abdullahi Ganduje
Asali: Twitter

"Yana da muhimmanci a sani cewa, Alhaji Muhuyi ya yi kwazon gaske wajen rike akalar jagorancin hukumar cikin nagarta daidai da yadda ka'idojin yaki da rashawa da kuma karbar korafe-korafen jama'a su ka yi tanadi."

KARANTA KUMA: Tallafin gwamnati saboda Coronavirus: An nemi buhuna 42 na kayan abinci an rasa a jihar Neja

Ganduje ya na mai cewa, Rimingado ya taka rawar gani matuka wajen sauya fasalin hukumar mai yaki da rashawa tare da fito da darajarta a fili ga idanun al'umma.

Gwamnan wanda ake yi wa lakabi da Khadimul Islama, ya ce hukumar ta yi kwazon gaske a wa'adin farko karkashin kulawar Rimingado ba tare da gwamnati ta yi ruwa ko tsaki ba.

Haka kuma Ganduje ya ce gwamnatinsa ta yaba da kwazon shugaban hukumar, musamman a bangaren tabbatar da masalahar zamantakewa, kare hakkin al'umma da kuma kwato hakkin gwamnati a hannun mahandama da 'yan babakere.

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tafiya a kan tsarin rashin tsoma hannu ko baki a cikin al'amuran hukumar wajen zartar da hukunce-hukuncenta bisa la'akari da bajintar da ta yi a baya.

Haka zalika Ganduje ya bukaci Alhaji Rimingado da ya sake zage dantsensa domin tabbatar da kwazon da ya yi a baya ya ninku a yanzu wajen yiwa jihar Kano hidima da kasa baki daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: