Covid-19: Ba zan saka dokar kulle a jihata ba - Gwamna Atiku Bagudu

Covid-19: Ba zan saka dokar kulle a jihata ba - Gwamna Atiku Bagudu

Gwamna Atiku Bagudu, ya ce ba zai saka dokar kulle a jihar Kebbi ba, inda ya ce za a bar jama'a su cigaba da sagaraftunsu na yau da gobe, amma dole su bi matakan kare kai daga kamuwa da yada cutar covid-19.

Bagudu ya bayyana hakan ne yayin taronsa da kwamitin ko ta kwana a kan annobar covid-19 a jihar Kebbi.

An yi taron ne a wata cibiyar lafiya da ke Kalgo a jihar Kebbi domin tattaunawa a kan tasirin matakan dakile yaduwar annobar covid-19 a jihar, kamar yadda jaridar 'The Nation' ta rawaito.

Gwamnan ya jinjinawa kwamitin a kan aikin da su ke yi tare da bayyana cewa gwamnati za ta cigaba da ba su duk hadin kai da gudunmawar da su ke bukata.

A cewar gwamnan, gwamnatin tarayya ta bawa jihar Kebbi motoci uku makare da kayan abinci da su ka hada da; buhun shinkafa 2,262, mai da sukari.

Kazalika, Bagudu ya sanar da cewa ministar walwala, jin kai da bayar da tallafi, Sadiya Umar Farouq, za ta ziyarci jihar Kebbi domin rabon tallafin gwamnatin tarayya ga talakawa da ma su karamin karfi.

Gwamnan ya bayyana cewa ya zuwa yanzu babu dokar kulle a jihar Kebbi, za a bar jama'a su gudanar da harkokinsu amma cikin tsari da biyayya ga matakan kare kai daga kamuwa da cutar coronavirus.

Covid-19: Ba zan saka dokar kulle a jihata ba - Gwamna Atiku Bagudu
Gwamna Atiku Bagudu da mamba a kwamitin yaki da annobar covid-19 a jihar Kebbi
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta hada kai da shugabannin addini da malamai domin daukar nauyin tafsiran watan azumi a gidajen radiyo da talabijin saboda gwamnatin tarayya ta hana taron jama'a.

Sai dai, kalaman gwamna Bagudu sun ci karo da sanarwar da gwamnoni, a karkashin kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), su ka fitar ranar Laraba.

DUBA WANNAN: El-Rufa'i ya saka sabuwar doka a Kaduna bayan warkewarsa daga cutar covid-19

A ranar Laraba ne rahotanni su ka bayyana cewa gwamonin jihohin Najeriya 36 sun amince da kaddamar da dokar kulle kasa baki daya har na tsawon sati biyu domin dakile yaduwar annobar covid-19.

Gwamnonin sun cimma wannan matsaya ne bayan sauraron bayanai daga gwamnonin jihohin Lagos, Bauchi, Oyo da Ogun a kan darussan da su ka koya daga yaki da annobar covid-19.

Shugaban kungiyar NGF, gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ne ya fitar da wannan sanarwa bayan kammala taron gwamnonin da aka gudanar ta hanyar amfani da fasahar kiran waya mai nuna bidiyo.

A cikin sanarwar, Fayemi ya bayyana cewa babu wanda za a yi wa uzuri sai ma su aiyuka ko bukatu na musamman.

Gwamnoni sun bukaci gwamnatin tarayya ta rage nauyin alhakin duba yaduwar annobar covid-19 daga wuyanta tare da dora shi a wuyan jihohi tunda yanzu ta yadu zuwa jihohi fiye da 25, sannan ta na cigaba da yaduwa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel