Tallafin gwamnati saboda Coronavirus: An nemi buhuna 42 na kayan abinci an rasa a jihar Neja

Tallafin gwamnati saboda Coronavirus: An nemi buhuna 42 na kayan abinci an rasa a jihar Neja

An karkatar da akalar tallafin gwamnati na buhunan kayan abinci 42 da aka tanada domin rarrabawa al'ummar unguwar Limawa da ke karamar hukumar Chachanga a jihar Neja.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, an yi sama da fadin wannan kayan abinci da gwamnati tayi tanadinsu a matsayin tallafi ga mabukata domin rage radadin da cutar coronavirus ta jefa su ciki.

Rahotanni sun bayyana cewa, bayan yin sama da fadin wannan tarin kayan abinci, ana kuma sayar da su a fili a babbar kasuwar garin Minna da ya kasance babban birnin jihar.

Kayan abincin da aka karkatar da akalarsu sun hadar da; buhunan Shinkafa 13; Gero 14; Masara 15 da kuma buhuna masu tarin yawa na Taliya.

Mataimakin shugaban karamar hukumar Chachanga wanda shi ma ya fito daga unguwar Limawa, Alhaji Saidu Njaga, ya gano wasu daga cikin kayan abincin da har an kasa su a kasuwa.

Bincike na tsanaki ya sanya aka gano cewa wasu daga cikin 'yan kwamitin da aka dora wa nauyin rarraba kayan tallafi su ne suka yi sama da fadin kayayyakin abincin na al'umma.

Tuni dai Alhaji Njaga ya ankarar da shugaban karamar hukumar, Alhaji Ibrahim Abubakar Bosso, a kan wannan lamari domin a ci gaba da bincike.

Gwamnan jihar Neja; Alhaji Abubakar Sani Bello
Gwamnan jihar Neja; Alhaji Abubakar Sani Bello
Asali: UGC

Tsananin takaici ya sanya ba tare da kafa wani kwamitin bincike ba, shugaban karamar hukumar ya gaggauta shigar da korafi har gaban gwamnan jihar, Alhaji Abubakar Sani Bello.

Baya ga gwamnan, Alhaji Bosso ya kuma kai kokensa kunnen shugaban kwamitin kula da cutar Covid-19 a jihar, wanda kuma ya kasance sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Ibrahim Matane.

KARANTA KUMA: Yanzu-Yanzu: Covid-19 ta hallaka mutane 2 a Legas

Alhaji Bosso yana neman gwamnatin jihar ta dauki mataki cikin gaggawa dangane da wannan lamari da ya misalta a matsayin zalunci tibiran.

Ana iya tuna cewa, gwamnatin jihar Neja ta bai wa Unguwar Limawa kula wa ta musamman biyo bayan samun wanda cutar coronavirus ta harba a yankin.

Kawo yanzu gwamnati ta killace dukkanin al'ummar yankin wanda adadin su ya kai kimanin 500 domin gano ainihin wadanda cutar ta harba don gudun bazuwarta a sauran sassan jihar.

Yayin da manema labarai suka tuntubi shugaban karamar hukumar ta Chanchanga domin jin ta bakinsa, Alhaji Bosso bai yi wata-wata ba wajen tabbatar musu da sahihancin rahoton.

Ya kara da cewa tuni har an kafa kwamitin gudanar da bincike domin zakulo dukkanin wadanda suka yi rub da ciki kan dukiyar da aka tanada domin talakawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel