Ji ka karu: Menene adadin lokacin da kwayar cutar Coronavirus take dauka kafin ta mutu?
A yayin da annobar Coronavirus ke cigaba da yaduwa, akwai bukatar jama’a su san iya lokacin da cutar ke dauka a wuraren da ake samun sa kafin ya mutu.
Majalisar lafiya ta duniya, WHO ta bayyana zuwa yanzu, annobar Coronavirus ta kama mutane fiye da miliyan 2, kuma ta kashe mutum 160,000 a duniya gaba daya.
KU KARANTA: Annobar Coronavirus: An samu mutuwar mutum na farko a jahar Oyo
Shugaban WHO, Tedros Ghebreysus ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru game da annobar a ranar Laraba a birnin Geneva, kasar Switzerland.
“A duniya gaba daya, mutane miliyan 2.5 ne cutar COVID-19 ta kama, kuma an samu mace mace 160,000 a dalilin ta.” Inji shugaban WHO, Tedros Ghebreysus.
Wannan ne tasa Legit.ng ta kawo muku jerin wasu wuraren da kwayar cutar Coronavirus mai toshe numfshi ta fi kwanciya da lokacin da take dauka kafin ta mutu, don kauce mata.
- Takarda: Kwayar cutar Coronavirus na daukan tsawon sa’o’i 3 kafin ta mutu
- Kayan sawa: Kwayar cutar Coronavirus na daukan tsawon sa’o’i 24 kafin ta mutu
- Bango: Kwayar cutar Coronavirus na daukan tsawon sa’o’I 36 kafin ta mutu
- Wayan karfe: Kwayar cutar Coronavirus na daukan tsawon kwanaki 3 kafin ta mutu
- Takardar kudi: Kwayar cutar Coronavirus na daukan tsawon kwanaki 4 kafin ta mutu
- Kofin/kwanukan tangaran: Kwayar cutar Coronavirus na daukan tsawon kwanaki 4 kafin ta mutu
- Cokula da kwanukan silba da na roba: Kwayar cutar Coronavirus na daukan tsawon kwanaki 7 kafin ta mutu
- Kyallen rufe fuska: Kwayar cutar Coronavirus na daukan tsawon kwanaki 7 kafin ta mutu
Duba da wadannan bayanai, ya zama dole jama’a su kasance masu kula da tsantseni wajen gudanar da al’amuransu na yau da kullum, musamman kula da tsaftar jikinsu da muhallinsu.
Ya kamata jama’a su dage da wanke hannuwa a kai a kai da soso da sabulu da ko sinadarin Sanitizer, kuma a kauce ma cudanya da shiga cikin dandazon jama’a idan ba ya zama dole ba.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng