Annobar Coronavirus: An samu mutuwar mutum na farko a jahar Oyo

Annobar Coronavirus: An samu mutuwar mutum na farko a jahar Oyo

Gwamnan jahar Oyo, Seyi Makinde ya sanar da samun mutuwar mutum na farko sakamakon annobar Coronavirus da ta kama shi a jahar, a ranar Laraba, 22 ga watan Afrilu.

Daily Trust ta ruwaito Makinde ya bayyana haka ne da misalin karfe 11:30 na daren Laraba a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Twitter.

KU KARANTA: Matan hafsoshin Sojan sama sun taimaka ma gajiyayyu da kayan abinci a Abuja

A cewarsa, mamacin ya mutu ne a babban asibitin koyarwa na jahar, University College Hospital Ibadan, tun ma kafin sakamakon gwajin da aka yi masa na cutar ya fito.

Sai dai ko bayan rasuwar tasa, da sakamakon gwajin ya fito, ya tabbatar mutumin yana dauke da annobar Coronavirus, kuma ita ce ta yi sanadiyyar mutuwarsa.

“Mun fara bin duk mutanen da ya yi mu’amala da su, kamar yadda aka ruwaito a jiya, mun mayar da wani mutumi dake dauke da cutar zuwa jahar Legas, don haka a yanzu mutane biyar ne kawai masu cutar a jahar Oyo.” Inji shi.

Annobar Coronavirus: An samu mutuwar mutum na farko a jahar Oyo

Gwamnan Oyo
Source: Twitter

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito jahar Oyo na da mutane 17 dake dauke da cutar Coronavirus, daga cikinsu guda daya ya mutu, an kuma mayar da wani zuwa Legas.

An kuma sallami wasu mutane 10 bayan sakamakon gwaji da aka musu guda biyu sun tabbatar basu dauke da cutar, a yanzu mutane biyar ne suka rage kacal masu dauke da cutar.

Don haka gwamnan ya shawarci jama’an su cigaba da zama a gidajen su, tare da bin dokokin da kwamitin yaki da cutar a jahar ta umarce su kamar wanke hannu da ruwa da sabulu.

Daga karshe ya nemi jama’a su kauce ma cakuduwa da jama’a da suka wuce mutane 10 a lokaci daya.

A wani labari kuma, Majalisar lafiya ta duniya, WHO ta ce zuwa yanzu, annobar Coronavirus ta kama mutane fiye da miliyan 2, kuma ta kashe mutum 160,000 a duniya gaba daya.

Shugaban WHO, Tedros Ghebreysus ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru game da cannobar a ranar Laraba a birnin Geneva, kasar Switzerland.

“A duniya gaba daya, mutane miliyan 2.5 ne cutar COVID-19 ta kama, kuma an samu mace mace 160,000 a dalilin ta.” Inji shugaban WHO, Tedros Ghebreysus.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel