Annobar Coronavirus: Gwamnan Gombe ya kaddamar da dokar ta baci a jahar

Annobar Coronavirus: Gwamnan Gombe ya kaddamar da dokar ta baci a jahar

Gwamnan jahar Gombe, Inuwa Yahaya ya sanya dokar hana shige da fice a fadin jahar daga karfe 6 na dare zuwa 7 na safe, har sai yadda hali yayi.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Laraba, inda yace ya dauki wannan mataki ne don kare yaduwar cutar Coronavirus a jahar.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus: Majalisar Musulunci ta Najeriya ta bayyana abin da ya kamata a yi da gawar Musulmi

Cikin sanarwar da ya fitar, Gwamna Yahaya ya ce dokar hana shige da ficen zai fara aiki ne daga karfe 6 na yammacin Alhamis, don haka ya nemi jama’an jahar su yi zaman su a gida.

Annobar Coronavirus: Gwamnan Gombe ya kaddamar da dokar ta baci a jahar
Annobar Coronavirus: Gwamnan Gombe ya kaddamar da dokar ta baci a jahar
Asali: Facebook

“Duk da matakan kandagarkin da muka dauka, amma ga shi muna fama da matsalolin cutar, don haka na sanya dokar hana shige da fice daga karfe 6 na dare zuwa 7 na safe daga ranar Alhamis, 23 ga watan Afrilu.

“Haka zalika mun dakatar da bude kasuwanni, tarukan siyasa, al’ada da na addini, tare da dakatar da duk wasu tafiye tafiye daga wani gari zuwa wani gari, don haka an kulle duk wasu tashoshin motoci da makarantun almajirai.” Inji shi.

Amma ya ce dokar ba ta shafi mutane dake gudanar da ayyuka na musamman ba, haka zalika yace nan bada jimawa za su fara mayar da almajiran dake jahar zuwa garuruwansu na asali.

Daga nan sai gwamnan ya umarci jami’an Yansanda su tabbata sun dabbaka umarnin ta hanyar kama duk mutumin da suka samu ya yi ma umarnin zaman gidan karan tsaye.

“Muna sane da matsalar da hakan zai haifar ga tattalin arziki da walwalar jama’a, don haka mun fara shirye shiryen raba kayan tallafi ga jama’a don rage musu radadin halin da za’a shiga.

“Mai martaba Sarkin Gombe ne zai jagoranci shugabancin kwamitin rabon tallafin ga jama’a, kuma kwamitin ne za ta tattaro kayayyakin da ake bukata a matsayin tallafin.” Inji shi.

Daga karshe gwamnan ya bayyana cewa za su fara feshi a zababbun unguwannin jahar, kuma ya yi kira ga jama’a su dage wajen sanya kyallen rufe fuska, wanke hannu da sabulu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel