Bayanin Ganduje a kan rahoton yawaitar mutuwar jama'a a Kano

Bayanin Ganduje a kan rahoton yawaitar mutuwar jama'a a Kano

Gwamnan jahar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi watsi da rahoton yawan mace-macen mutane a Kano, inda ya bayyana batun a matsayin jita-jita.

Ya ce alkaluman adadin mutanen da aka tattaro daga makabartun cikin birni Kano bai yi ko kusa da adadin da rahoton ya yi ikirarin cewa sun mutu ba.

Da ya ke jawabi a wata tashar talabijin, gwamnan ya bayyana cewa, “Shakka babu, mun gani a shafin farko na jaridar Daily Trust, amma ina mai ba ku tabbacin cewa labarin ba gaskiya bane. Jita-jita ne kawai.”

Bayanin Ganduje a kan rahoton yawaitar mutuwar jama'a a Kano

Bayanin Ganduje a kan rahoton yawaitar mutuwar jama'a a Kano
Source: Twitter

Gwamnan ya yi bayanin cewa binciken da aka gudanar a fadin kananan hukumomi uku ya nuna sabanin abin da jaridar ta wallafa.

“Daga ranar 19 ga watan Afrilu zuwa yanzu, mun gano cewa mutane uku ne kadai suka mutu a karamar hukumar Gwale, daga karamar hukumar birnin Kano mun gano cewa mutane bakwai ne suka mutu.

"Sannan daga Kumbotso, mun gano cewa mutane uku ne kawai suka mutu.

“Toh kun gani kenan idan muka hada jimillar adadin mutanen gaba daya, basu yi ko kusa da adadin mutanen da ake ikirarin cewa sun mutu ba.

"Don haka abunda muke fada mu ku, kuma mu ke so ku fahimta shine, "wannan labarin jita-jita ne kawai.

“Abinda ya fi muhimmanci shine batun cewa mun dauki mataki cikin gaggawa.

"Kamar yadda kuka sani, kafin wannan lokacin, bamu da masu daukar rijista a makabartunmu.

"Amma saboda wannan labari, mun yanke shawarar sauya tsari, don a yanzu haka mu na da mutane a makabartu da za su dinga bamu bayani a kan adadin mutanen da suka mutu da kuma abunda ya haddasa mutuwarsu," a cewarsa

Gwamnan ya kuma bayyana cewa mutum daya ne kawai ya mutu daga COVID-19 a jahar.

Ganduje ya ce ya aminta cewa Kano babban birni ne kuma ana iya samun wadanda za su mutu kamar dai a kowanne birni na duniya, amma ya ce lallai “ba mu samu karin wadanda suka mutu ba daga annobar covid-19 ba.”

Ya nuna rashin jin dadinsa a kan adadin mutanen da aka tabbatar suna da cutar covid-19 a jahar.

KU KARANTA KUMA: Ganduje ya sasauta dokar kulle a Kano

Ya kara da cewa adadin ma su cutar ya fara hauhawa ne saboda karuwar gwaje-gwaje da ake gudanarwa sakamakon samar da cibiyar gwajin kwayar cutar covid-19 a jahar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel