Kano: Ganduje ya yi magana a kan dage dokar hana zirga-zirga

Kano: Ganduje ya yi magana a kan dage dokar hana zirga-zirga

- Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa akwai yuwuwar a dage dokar hana zirga-zirga a jihar

- Gwamnan ya ce za a yi hakan ne don bai wa jama'ar jihar damar yin siyayyar watan Ramadan mai kamawa a ranar Juma'a

- Kamar yadda gwamnan ya bayyana, kullum kara yaduwa cutar ke yi a jihar don haka babu amfanin dage dokar hana zirga-zirgar

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa a shirye yake da ya ba jama'ar jihar damar zuwa siyayyar azumin watan Ramadan.

Gwamnan ya ce: "Akwai yuwuwar mu bai wa jama'a koda sa'o'i kadan ne don samun damar siyayyar azumi saboda watan Ramadan da zai iya kamawa a ranar Juma'a."

Gwamna Ganduje wanda ya zanta da The Cable ta jihar Legas, ya bayyana cewa: "A kullum masu ciwon karuwa suke a jihar Kano. Don haka babu bukatar dage dokar hana zirga-zirgar a yanzu".

A daren Talata ne ma'aikatar lafiya ta jihar Kano ta tabbatar da cewa mutum 73 ne ke dauke da cutar Covid-19 a jihar.

Kano: Ganduje ya yi magana a kan dage dokar hana zirga-zirga
Kano: Ganduje ya yi magana a kan dage dokar hana zirga-zirga
Asali: Facebook

KU KARANTA: Shugabanin APC na jihohi sun bayar da shawarar yadda za a zabi magajin Abba Kyari

A wani labari na daban, an ji cewa almajirai guda 419 ne gwamnatin jihar Katsina ta karba daga hannun gwamnatin jihar Kano da aka bukaci su koma jihohinsu na haihuwa a yunkurin Kano ke yi na takaita yaduwar Covid-19.

Direktan watsa labarai na ofishin sakataren gwamnatin jihar Katsina, SGS, Alhaji Abdullahi Yar’adua ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya raba wa menama labarai a ranar Laraba a Katsina.

Sanarwar ta jadadda cewa SSG, Alhaji Mustapha Inuwa ya karbi almajiran ne a madadin gwamnatin jihar Katsina kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

An ruwaito cewa an jiyo inuwa yana bayyana farin cikinsa kan yadda jihohin Katsina da Kano ke daukan matakai iri daya domin takaita yaduwa cutar da coronavirus a jihohinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel