COVID-19: Zai yi wuya a bai wa 'yan Najeriya wutar lantarki kyauta - Minista

COVID-19: Zai yi wuya a bai wa 'yan Najeriya wutar lantarki kyauta - Minista

- Ministan wutar lantarki na kasa, Saleh Mamman ya ce batun bai wa 'yan Najeriya wuta na watanni biyu kyauta, ba abu ne mai yiwuwa ba

- Ya ce duk wata kamfanonin wutar lantarki na karbar naira biliyan 50 daga hannun jama'a, don haka gwamnati ba za ta iya biyan biliyan 100 na wata biyu ba

- Mamman ya kuma ce yan Najeriya iri biyu ne akwai masu kudi akwai talaka, don haka wa za a ba, wa kuma za a hana

Ministan wutar lantarki na Najeriya, Saleh Mamman, ya ce batun da ake yi na yiwuwar bai wa al’umman kasar wutar lantarki kyauta har na tsawon watanni biyu, ba abu ne mai yiwuwa ba.

Ana dai ta kiraye-kiraye ga gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan ta yafe wa ‘yan kasar kudin wuta saboda dokar hana fita da aka sanya a kasar.

COVID-19: Zai yi wuya a bai wa 'yan Najeriya wutar lantarki kyauta - Minista

COVID-19: Zai yi wuya a bai wa 'yan Najeriya wutar lantarki kyauta - Minista
Source: UGC

Ministan ya bayyana cewa: "A kowani wata kamfanonin wutar lantarki na karbar naira biliyan 50 daga hannun jama'a, saboda haka gwamnati ba za ta iya biyan na wata biyu ba wanda ya ke naira biliyan 100”, shashin Hausa na BBC ya ruwaito.

Mamman ya kara da cewa "'Yan Najeriya suna suka tara, saboda akwai masu halin da ke zaune a Maitama da Asokoro, sannan kuma akwai talakawa a kauyuka, toh wa za a bai wa, wa za a hana?"

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Nasarawa ta saki fursunoni 115, ta ba kowannen su N5,000

'Yan majalisar Najeriya ne dai suka nemi da a bai wa 'yan kasar damar shan wuta kyauta har ta tsawon watanni biyu, domin samun sukunin zaman gida yayin da gwamnati ta sa dokar hana zirga-zirga.

A wani labari na daban, mun ji cewa shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin biyan albashin lakcarorin jami'a da suka yiwa gwamnati bore ta hanyar kin rijista kan manhajar IPPIS.

Shugaban kasan ya ce a biyasu ne bayan ganawar da yayi da ministan kwadago da aikin yi, Sanata Chris Ngige, jiya a Abuja.

Gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami'o'in Najeriya sun dade da shiga takun tsaka kan lamarin rijista kan manhajar biyan albashi na zamani wato IPPIS.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel