Jihohi 25 da aka samu bullar cutar Covid-19 a Najeriya - NCDC

Jihohi 25 da aka samu bullar cutar Covid-19 a Najeriya - NCDC

A yayin da hukumomin lafiya ke ci gaba da aiki tukuru domin hana yaduwar cutar coronavirus a Najeriya, cutar tamkar wutar daji na ci gaba da bazuwa a kasar.

A halin yanzu an samu bullar cutar covid-19 a jihohi 25 na Najeriya ciki har da babban birnin tarayya kamar yadda alkaluman cibiyar dakile yaduwar cututtuka a kasar NCDC suka tabbatar.

Taskar bayanai ta NCDC a ranar Laraba, 22 ga watan Afrilun 2020, ta ce cutar corona ta harbi mutane 782 yayin da tuni mutane 197 suka samu waraka.

Ya zuwa yanzu dai mutane 25 cutar ta hallaka a fadin Najeriya kamar yadda kididdigar alkaluman ta tabbatar.

Ga jerin adadin mutanen da suka kamu da cutar a kowace daya daga cikin jihohi 25 na Najeriya da cutar ta bulla:

Lagos-430; Abuja-118; Kano-73; Osun-20; Ogun-20; Oyo-16; Katsina-16; Edo-15; Kwara-9; Kaduna-9; Akwa Ibom-9; Borno-9; Bauchi-8; Gombe-5; Delta-4; Ekiti-4; Ondo-3; Rivers-3; Jigawa-2; Enugu-2; Niger-2; Abia-2; Benue-1; Anambra-1; Sokoto-1.

Da misalin karfe 11.25 na daren ranar Talata, cibiyar mai fafutikar dakile yaduwar cututtuka ta sanar da cewa an samu karin mutane 117 da cutar covid-19 ta harba a fadin Najeriya.

KARANTA KUMA: Fargabar kamuwa da cutar corona ya sa Likitoci sun bari wata mata ta mutu a Enugu

Jihohin da cutar ta bulla karo na farko a baya-bayan nan sun kasance Borno da Gombe a yankin Arewa maso Gabas, jihar Sakkwato a Arewa maso Yamma da Abia a yankin Kudu maso Gabas.

Jihar Legas ce a kan sahu na gaba ta fuskar yawan wadanda cutar ta harba, sai kuma birnin Abuja a mataki na biyu yayin da jihar Kano ta biyo bayansu.

Taswirar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta tabbatar cewa jimillar mutane da cutar ta harba ta kai 2,580,729 inda jimillar wadanda suka mutu kuma ta kai 178,371.

A rahoton da muka samu daga sashen Hausa na BBC, mun ji cewa an dakatar da gwajin gano masu cutar corona a jihar Kano saboda rashin wadatattun kayan aiki.

A ranar Talata ne dai gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, ya nemi gwamnatin tarayya da ta kawo masa dauki na tallafin kudi domin saukaka radadin yakar wannan annoba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel