Farashin danyen mai na Najeriya ya karye zuwa $19.71 a kasuwar duniya

Farashin danyen mai na Najeriya ya karye zuwa $19.71 a kasuwar duniya

Gabanin rufe kasuwa a Yammacin jiya na Talata, farashin danyen man fetur a duniya yayi mummunar faduwar ta bai taba makamancinta ba tsawon shekaru 18 da suka gabata.

Tabbas annobar cutar corona ce ke da alhakin disashewar kasuwar man fetur a duniya, lamarin da ya kara dugunzuma hankalin kasashen duniya.

Farashin danyen mai nau'in West Texas Intermediate na kasar Amurka, a ranar Litinin ya yi faduwar da ya kasance tamkar ana neman kai da shi, wanda hakan bai taba faruwa ba a tarihi.

Hakan ya sanya farashin danyen mai nau'in Brent Crude ko kuma London Brent irin wanda Najeriya ta azurta da shi, ya karye raga-raga.

A halin yanzu ana sayar da Brent Crude a kan dalar Amurka 19.71 na kowace ganga guda a kasuwar duniya.

Alkaluma sun tabbatar shi ne mafi kankantar farashin da aka sayar da wannan nau'i na mai a tsawon shekaru 18 da suka gabata.

Annobar corona ita ce sanadiyar faduwar farashin man fetur a duniya sanadiyar yadda al'amuran gudanarwa a kowace kasa suka tsaya cik.

Hakika an rasa masu sayan man fetur saboda yadda masana'antu da kamfanoni suka daina aiki, yayin da rumbunan ajiyarsa suka cika maki kuma babu mabukatansa.

Matatar Danyen mai ta Dangote

Matatar Danyen mai ta Dangote
Source: UGC

Masu lura da tattalin arziki sun tabbatar da bushewar kasuwar man fetur, kuma bukatarsa ta ragu yadda ba a tunani a yayin da duniya ta kasance kusan a kulle babu fita.

Ana iya tuna cewa a farkon watan Afrilu ne mambobin kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC, suka amince a kan rage yawan man fetur da kowace kasa za ta rika fitarwa kasuwa.

OPEC ta yanke wannan hukuncin ne domin farfado da darajar man fetur a kasuwannin duniya.

Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan lamari zai haddasa tabarbarewa tattalin arzikin Najeriya a sanadiyar yadda faduwarsa ta sauya hasashen da kasar tayi a cikin kasafin kudinta na bana.

Gwamnatin Najeriya ta dogara da arzikin man fetur wajen samun kashi 90% na kudaden shigarta a hasashen da tayi cikin kasafin kudin bana.

Gwamnatin kasar tun a watan Dasumba na 2019 yayin shigar da kasafin kudinta na bana, ta kiyasta farashin man fetur a kan $57 a duk ganga.

Daga bisani bayan da annobar corona ta dagula al'amura, ministar kudin, kasafi da tsare-tsaren Najeriya, Zainab Ahmed, ta sanar da rage fiye da Naira biliyan 320 daga kasafin kasar na bana.

Sabanin yadda majalisar ta amince a baya, a yanzu an kiyasta farashin man fetur a kan $30 na kowace ganga. Yanzu kuma da lamurra suka ci gaba da tabarbarewa dole ne kasar ta sake nazari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel